Wata tawaga daga hukumar lura da jami’o’in kasa wato NUC ta kai ziyarar tantancewa a jami’ar Franco-British International University dake ...
Wata tawaga daga hukumar
lura da jami’o’in kasa wato NUC ta kai ziyarar tantancewa a jami’ar Franco-British
International University dake Kaduna.
Tawagar wacce ke karkashin
jagorancin Mataimakin Darakta, a bangaren lura da Babban shiri da samar da kayayyakin
da ake so, Dr. Mustapha Rasheed, ta isa Kaduna ne a ranar Asabar 28 ga watan
Janairu, 2023, domin tantance kayan aikin da aka tanada a jami’ar da ake
yunkurin samarwa.
Kayayyakin da tawagar ta
ziyarta sun hada da dakunan karatu da manyan dakunan taruka, dakunan
gwaje-gwaje, dakunan ajiye littafai, ofisoshin ma’aikata da kuma dakunan kwanan
dalibai da wuraren ma’aikata.
Tawagar ta samu tarba ne
bayan ta isa wurin daga wanda yake son samar da Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar
Gwarzo tare da kwamitin tsare-tsare da aiwatarwa wanda suka dukufa wajen ganin
jami’ar da ake son a kafa ta samu shawarwari daga NUC domin ganin an ba ta
lasisin soma aiki a matsayin jami’a mai zaman kanta a Nijeriya cikin kankanin
lokaci.
A ziyarar da tawagar ta kai
Jami’ar FBI da ke Cibi Close ta hanyar Nnamdi Azikiwe Expressway a Kaduna, ta
zagaya lungu da sako na Jami’ar baya ga ziyartar wasu muhimman wurare a wannan
jami’ar.
Bayan tantance kayayyakin
aikin, tawagar ta NUC da membobin kwamitin Tsare-tsare da aiwatar da Jami’ar a
karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Abubakar Kankia sun yi zama inda aka
tattauna kan manyan sakamakon binciken da kuma bayar da shawarwari masu ma’ana.
Sauran jami’an hukumar ta
NUC sun hada da Engr. Sulaiman Adebayo, Mataimakin Darakta a ofishin Darakta,
Malam Abubakar Nuhu, mataimakin Darakta kan harkokin ilimi, Barista Ummukultum
Giwa, Mataimakiyar Darakta kan sha’anin mulki da shari’a, da Lola Agawo, ma’aikacin
Sakatare.
Jami’ar Franco-British
International, Kaduna na daya daga cikin Jami’o’i hudu da Farfesa Adamu
Abubakar Gwarzo ya kafa.
No comments