Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kulle Makabartar Garin Samaru: Daga Karshe An Cimma Matsaya

Daga Idris Umar   A sakamakon shiga mawuyacin hali da  al'ummar garin Samaru da kewaye dake karamar hukumar Sabon Gari Zariy...


Daga Idris Umar 

A sakamakon shiga mawuyacin hali da  al'ummar garin Samaru da kewaye dake karamar hukumar Sabon Gari Zariya suka shiga na rashin makabarta inda ake rufe bayin Allah idan rai ya yi halinsa. Hakan ya sa suka rubuta koke ga shugaban karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna Honorabul Injiniya Muhammad Usman da ya yi wa Allah ya yi wa Annabinsa yasa baki akan matakin da hukumar soja ta dauka na killace sabuwar makabarta da suka yi da katanga da umurnin ka da wani ya kara shiga balle zuwa binne gawa yayin da wani ya mutu a wannan makabarta.

Hakan yasa shugaban karamar hukumar ya kafa kwamiti da zai karbi wannan koken zuwa ga babban ofishin soji na kasa dake Abuja.

Tuni majiyarmu ta sami labarin wani babban soja da mahaifinsa ke kwance a wannan makabartar ya sami labarin halin da mutanen Samarun ke ciki a lokaci mai tsawo. Majiyarmu ta sami tabbacin wannan babban Sojan kuma bawan Allah ya karbi koken shugaban karamar hukuma da jama'ar garin Samaru zuwa ga ofishin Babban Hafsan sojan kasa na Nijeriya hakan yasa yanzu haka an sami matsaya mai tushe tare da bude makabartar karkashin kulawar karamar hukumar ta Sabon Gari.

A ranar Litinin 2/1/23 babban Hafsan sojojin na kasa ya turo wakilansa don zama da shugaban karamar hukumar Sabon Gari Honorabul Mohammed Usman domin ganin an samarwa alu'mma mafitar da ya dace, don ci gaba da bizne mutane a wannan makabarta tuni jama'ar garin Samaru da kewaye suka shiga murna da samun wannan ci gaba.

Wakilinmu ya zanta da shugaban karamar hukumar ta Sabon Garin Honorabul Muhammad Usman jim kadan bayan sun gama tattaunawa da wakilin babban Hafsan sojan kasa da yazo da jama'arsa.

Shugaban karamar hukumar ya ce wannan nasara daga Allah yake kuma ya nuna jin dadinsa ganin yadda hukumar sojojin suka bada goyon baya akan lamarin.

Karshe yabyi Jan hankali akan masu yada jita-jita game da lamarin maganar makabartar ya ce suji tsoron Allah. Shugaban ya ce yanzu zai kafa kwamiti mai karfi da zai lura da maganar ci gaba da bizne mutane a wannan makabartan karkashin doka da oda.

Ya ce yanzu haka akwai maganar kara fadin makabartar da ake yi tsakanin hukumar sojoji da karamar hukumar ta su. Amma yanzu duk lokacin da aka yi rasuwa to akwai wanda za a karbi makulli a wajensu don bude kofar makabartan kafin kammala tsare-tsare dake kasa.

Daga cikin manyan mutanen da suka jagoranci zuwa bude wannan makabartan a wannan lokaci akwai shi kanshi shugaban karamar hukumar ta Sabon Gari Honorabul Muhammad Usman da Honorabul Isa Hazo Dan majalisar jiha mai wakiltar Basawa da Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo sai Sarkin Hayin Dogo Alhaji Shehu da Kansiloli da Limamai da Fastoci da masu Anguwanni da wakilan rundunar soja ta kasa da suka zo daga Abuja da Barikin Basawa.

No comments