Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masarautar Zazzau Ta Ce Za Ta Bi Diddigi Wajen Ganin An Hukunta Dogarinta Da Ya Yi Wa Wata Mata Fyade

Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamali, ya bayar da umarnin korar wani Dogarinsa mai suna Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa, wanda ake ...


Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamali, ya bayar da umarnin korar wani Dogarinsa mai suna Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa, wanda ake zarginsa da jagorantar wasu wajen yi wa wata mata fyade a Zariya dake jihar Kaduna.

Dogarin wanda yanzu aka kora ya yaudari wata mata da ta zo neman taimako a wajen Sarki ta hannunsa, domin a tallafa mata kan auren da za ta yi.

Majiyarmu ta rawaito cewa, maimakon ya kai matar wajen sarki kai tsaye, sai ya kai ta wani wuri tare da wasu abokansa, inda suka yi ta mata fyade.

A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin yada labarai da hulda da jama’a na sarkin, mai dauke da sa hannun wani Abdullahi Aliyu Kwarbai, majalisar ta umurci ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Lamarin ya faru ne a lokacin da dogarin ya yaudari matar da ke shirin daurin aure, inda ta zo neman taimako daga wajen Sarkin ta hanyarsa.

“Maimakon Rimin Tsiwa ya kai matar wurin sarki, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, sai ya kai ta wani wuri shi da abokansa suka yi mata fyade.”

Majalisar ta yi alkawarin bin diddigin lamarin har sai an yi adalci.

Wasu bayanai sun tabbatarwa da Jaridar MADOGARA cewa matar wacce ta Musulunta ta ta6a aure, a halin yanzu wani auren za ta sake yi shi ne ta zo masarautar Zazzau ganin Sarki domin neman taimako.

Majiyarmu ta ce tuni rundunar 'yan sanda suka cafke mutum biyu cikin wadanda ake zargi domin ganin an gurfanar da su a gaban kotu.

No comments