Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Bukatar A Gaggauta Biyan CBN Bashin Naira Tiriliyan 22 – Shugaba Buhari

  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta sake duba matsayar ta kan kudirinsa na ganin gwamnatin tarayya ta b...

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta sake duba matsayar ta kan kudirinsa na ganin gwamnatin tarayya ta biya babban bankin Najeriya bashin naira tiriliyan 22.7.

Buhari na bayyana hakan ne, lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 a zauren gamayyar majalisun dokokin kasar.

Shugaban ya yi gargadin cewa rashin amincewar majalisar, zai haifar da karin kudin ruwa zuwa naira tiriliyan 1.8 a shekarar 2023 kuma Najeriya za ta dauki tsawon shekaru 40 ta na biyan bashin.

Bukatar ta Buhari na zuwa ne mako guda bayan Majalisar Dattawa ta ki amincewa da bukatarsa na sake fasalin yadda za a yi amfani da naira tiriliyan 22.7.

Da yake jawabi a wajen rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2023, shugaban ya bayyana cewa jimillar kudaden da aka warewa ayyukan raya kasa na naira tiriliyan 21.83 an kara naira tiriliyan 1.32 a kan kudirin farko na naira tiriliyan 20.51.

Buhari ya ce akwai bukatar ayi gaggawar biyan babban bankin kasar wannan bashi domin kaucewa karuwar kudin ruwa da za a dauki shekaru da dama kafin a gama biyan sa.

No comments