Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mutum 500 Uba Sani Win Project Da Uba Sani Actualization Project Suka Bai Wa Tallafin Magani A Zariya

Daga Fatima Idris Zariya UBA SANI WIN PROJECT da UBA SANI ACTUALIZATION PROJECT sun gabatar da bayar da tallafin bayar da magani...


Daga Fatima Idris Zariya

UBA SANI WIN PROJECT da UBA SANI ACTUALIZATION PROJECT sun gabatar da bayar da tallafin bayar da magani a garin Dogarawa dake a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna. Wakiliyarmu ta halartar taron.

Taron an gudanar da shi ne a makarantar Junior Secondary dake Anguwar Dogarawa inda dubban mutane suka sami halarta. Kwamared Muktar Zubair shi ne shugaban wannan tafiyar ta UBA SANI WIN PROJECT.

Yayin da yake kaddamar da bayar da magani ga al'ummar Dogarawa ya bayyana cewa suna bayar da tallafin ne don taimakon jama'a kamar yadda suka saba yi a lokutan baya karkashin tafiyar Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023 in Allah ya kaimu.

Kwamared Muktar ya sha alwashin ci gaba da irin wannan hidima ga jama'a zarar an ba mai gidansu goyon baya a zabe mai zuwa da ikon Allah. Karshe ya yi matukar farin ciki bisa yadda jama'a suka bashi goyan baya tare da amsa kiran da ya yi masu.

Dakta Zaid Abubakar shi ne Uban wannan tafiya shima ya sami zuwa wajen taron har ya sanyawa taron albarka tare da nuna goyon baya da fatan alheri ga tafiyar.

Shima Sarkin Dogarawa Alhaj Ahmed Usman ya sami zuwa wajan taron kuma ya yi wa Kwamared Muktar Zubairu fatan alheri da ya kawo wa jama'ar garin Dogarawa tallafin magani.

Wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli Barista Ishak wakilin Yarbawan Zazzau shima godiya ya yi da kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan abin alherin da UBA SANI WIN PROJECT ta kawo ma jama'ar garin Dogarawa.

Dakta Tajuddin shi ne shugaban ayarin likitoci masu kula da harkar lafiya a tafiyar Dan takarar gwamnar jihar Kaduna shima ya gamsu da yadda UBA SANI WIN PROJECT suke gudanar da bayar da tallafin ga jama'a har ya yi fatan Allah ya bai wa Dan takarar nasara.

Bincike ya tabbatar da cewa akalla mutum 500 ne za su amfana da tallafin maganin.

Haka zalika tallafin ya shafi gwaje-gwaje ne a bangarorin da dama tare da bayar da magani bayan tabbatar da irin lalurar dake damun wanda aka gwada. Malam Sani daga Anguwar ta Dogarawa na daya daga cikin wanda aka gwada har aka bashi magani shima ya yi wa Dan takarar fatan samun nasara. An kaddamar cikin tsari da nasara.

No comments