Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nura Soro Ya Rabawa Membobin Jam'iyyar APC Naira Miliyan 86 A Jihar Bauchi

A shekaranjiya ne Mallam Dr. Nura Manu Soro, Kodinetan kamfen na Tinubu/Kashim na jihar Bauchi ya fara rabon kudi ga jagororin j...


A shekaranjiya ne Mallam Dr. Nura Manu Soro, Kodinetan kamfen na Tinubu/Kashim na jihar Bauchi ya fara rabon kudi ga jagororin jam'iyyar APC na jihar Bauchi domin neman goyon bayan al'umma  kan nasaran jam'iyyar APC a jihar Bauchi. 

Nura Manu Soro ya sha alwashin samun nasaran jamiyyar APC a matakin kasa da jiha a Bauchi yayin zaben shekarar 2023.

Nura Manu Soro ya ce wannan kudi somin tabi ne yanzu za a shiga hidimomin kai tsaye domin samun nasara jam'iyyar APC a jihar Bauchi.

Ya fara  zaman shi da Ciyamomin jam'iyyar APC daga matakin karamar hukuma zuwa gunduma na duk kananan hukumomin jihar Bauchi guda 20.

Nura Manu Soro ya tabbatar da cewa ba su shakkan samun nasarar jam'iyyar APC a Bauchi domin haka jam'iyyar za ta ci gaba da tallafa ma al'umma za a shiga zabe cikin walwala.

No comments