Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shinkafi ya gargadi Iyayen masu yi wa 'Yan Bindiga fataucin makamai a Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Mamuda Aliyu Shinkafi ya gargadi Iyayen masu yiwa 'yan Bindiga fataucin ...



Daga Hussaini Ibrahim

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Mamuda Aliyu Shinkafi ya gargadi Iyayen masu yiwa 'yan Bindiga fataucin makamai a Zamfara da su daina wannan muguwar sana'a ko su gamu da fushin gwamnati.

Shinkafi ya bayyana haka ne a wajen yakin neman zaben na Jam'iyyar APC a Karamar hukumar Maradun.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa, Jihar Zamfara ta yi kaurin suna wajen safarar miyagun makamai ga 'yan taadda da suka addabi yankinmu don harda ga wasu jihohin ana zuwa Zamfara sayan makamai, in ji Shinkafi. 

Shinkafi ya kuma ya jaddada cewa, iyayen wadanda suka san 'ya'yansu na cikin wannan muguwar sana'a da su dakatar da su don gwamnati ba za ta kyalesu ba.

"Don duk kokarin da gwamna Matawalle ya yi akan sulhu da 'yan ta'adda amma abun ya ci tura, dan haka tura takai bango, idan kunne ya ji jiki ya tsira, inji Tsohon gwamna, Shinkafi.

Shi kuwa takwararsa, tsohon gwamna Abdul'aziz Yari kuma Dan takarar Sanata ta Yamma, ya tabbatar da cewa, za su hada  kai wajen yaki da 'yan bindiga kafin zabe za su tarwatsa duk wata maboyarsu da ke fadin jihar ta Zamfara. Don haka batun sulhu ya kare ga duk wani Dan ta'adda da ke cikin Jihar ta Zamfara.

A nasa jawabin, Gwamna Bello Matawalle mai neman kujerar gwamna karo na biyu ya tabbatar da cewa, batun Yaki da 'yan ta'adda babu gudu babu ja da baya dan sai da tsaro da zaman lafiya al'umma ke ci gaba, inji gwamna Matawalle.

"Don haka da zarar kun zabe mu a zaben mai zuwa da yardar Allah wannan ta'addancin zai zo karshe kuma yanzu haka kafin zabe za ku ga abin da zai faru ga su 'yan ta'addan, inji gwamna Matawalle.

Gwamna Matawalle ya kuma nemi alfarmar al'ummar jihar Zamfara da su zabi 'yan takarar Jam'iyyar APC a matakin Shugaban Kasa da 'yan Majailisar Dattawa da na Wakilai da na Gwamna da 'Yan Majalisar Dokoki Jihar don ci gaba da ayyukan da suka dauko na ci gaban Jihar ta Zamfara.

No comments