Manyan kasashe na ci gaba da jajantawa tare da alkawarta taimakawa kasashen Turkiya da Syria yayinda tuni taimakon wasu ya fara isa ga kas...
Manyan kasashe na ci gaba da jajantawa tare da alkawarta taimakawa kasashen Turkiya da Syria yayinda tuni taimakon wasu ya fara isa ga kasashen biyu makwabtan juna, bayan girgizar kasa mafi muni mai karfin maki 7.8 da ta afka musu wadda zuwa yanzu ta kashe fiye da mutane dubu 4 da 300.
Girgizar kasar wadda ta faru har sau biyu a kasashen na Turkiya da Syria da farko anga afkuwar mai karfin maki 7.8 kafin daga bisani a sake samun mai karfin maki 7.6, inda zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da dubu 4 da 300 tare da rushe gidajen da suka haura dubu 5 da 600 yayinda aka yi nasarar zaro mutane dubu 7 da 840 da ransu daga baraguzan gine-gine.
Wasu daga manyan kasashen da tun a jiya suka alkwarta taimakawa kasashen biyu sun fara shigar da agajinsu kasashen biyu da ke fuskantar ibtila’in mafi muni cikin fiye da karni 7.
Tuni aka fara ganin kayakin agaji da jami’an kai dauki daga kasashe da kunhiyoyi ciki har da Tarayya Turai da NATO da Amurka da Japan da Birtaniya da kasashen yankin Gulf da kuma Rasha baya ga Iran, yayinda Korea ta kudu ta alkawarta isowar nata kayakin agajin.
A bangare guda shugaba Joe Biden wanda tawagar jami’ansa ke kasashen biyu ya nanata cewa Amurka za ta taimakawa Turkiyya da dukkanin abin da ta ke bukata a wannan yanayin.
Yanzu haka dai an samar da matsugunan wucin gadi ga miliyoyin mutane da wannan ibtila’I ya shafa akan iyakokin kasashen biyu.
No comments