Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Buhari Ya Kafa Kwamitin Mika Mulki Ga Magajinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kwamitin Mika Mulki domin saukaka wa gwamnatinsa shirye-shiryen mika mulkin ga wanda z...


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kwamitin Mika Mulki domin saukaka wa gwamnatinsa shirye-shiryen mika mulkin ga wanda zai gaje shi a wannan shekara ta 2023.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da haka a birnin Abuja a wannan Alhamis, yayin da mambobin kwamitin suka hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da Babban Lauyen Gwamnati kuma Sakataren din-din-din a Ma’aikatar Shari’a.

Kazalika kwamitin ya kunshi Sakatarorin din-din-din na Ma’aikatar Tsaro da ta Harkokin Cikin Gida da ta Kudade da Kasafi.

Ha ila yau, kwamitin ya kunshi Sakatarorin din-din-din na ma’aikatun Harkokin Waje da ta Yada Labarai da Al’adu da kuma Ma’aikatar Birnin Tarayya Abuja.

Za a kaddamar da wannan kwamitin ne a ranar Talata, 14 ga watan Fabairun da muke ciki da misalin karfe 12 na rana agogon kasar a dakin taro na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a birnin Abuja.

Ana sa ran daukacin mambobin su hallara da kansu ba tare da tura wakili ba kamar yadda wata sanarwar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta sanar.

Shugaba Buhari ya sha nanata cewa, zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2023.

No comments