Gwamnan Kano dake Najeriya Abdullahi Ganduje ya maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kotun koli inda yace bashi da hurumin yin gaban ...
Gwamnan Kano dake Najeriya Abdullahi Ganduje ya maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kotun koli inda yace bashi da hurumin yin gaban kansa wajen sauya takardun kudaden naira ba tare da tintibar majalisar ministocinsa da majalisar tattalin arzikin kasa ba.
Ganduje ya bukaci kotun koli ta soke shirin Buhari na sauya kudin kamar yadda Babban Bankin Najeriya ya fara aiwatarwa wajen janye takardun kudin naira 200 da 500 da kuma 1,000 wanda yace ya haifarwa mutane sama da miliyan 20 dake cikin Kano matsaloli da dama.
Gwamnan ya kuma bukaci kotun koli da ta umurci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da ci gaba da aiwatar da shirin saboda yadda ya sabawa tanade tanaden kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da ake amfani da shi.
Har ila yau Ganduje ya kuma bukaci kotun kolin da ta tilastawa gwamnatin tarayya bada umurnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin da aka janye, tare da bayyanawa karara cewar shugaban kasa bashi da hurumin daukar irin wadannan matakai ba tare da gabatar da su ga majalisar ministoci da kuma majalisar tattalin arzikin kasa ba.
Gwamnan ya nemi kotun da ta bayyana cewar umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa Babban Bankin kasar na aiwatar da shirin haramcacce ne kuma ya saba ka’ida.
Ga alama dai tsuguni bata karewa gwamnatin tarayyar Najeriya akan wannan Shirin ba, ganin yadda ake ci gaba da samun masu adawa da Shirin na fitowa bainar jama’a, bayan da wasu gwamnoni 3 suka shigar da kara inda suke bukatar tsawaita lokacin aiwatar da shirin.
Kotun kolin dai ta baiwa babban bankin umurnin ci gaba da shirin sauya kudin har zuwa lokacin da zata yanke hukuncin akan karar da wadancan gwamnoni 3 suka shigar.
No comments