Daga Idris Umar, Zariya Hausawa sun ce ka yi dan zamba ne hakan ta faru a garin Samaru ta karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kad...
Daga Idris Umar, Zariya
Hausawa sun ce ka yi dan zamba ne hakan ta faru a garin Samaru ta karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.
Saura kwana 3 zaben shugaban kasa bisa shugaban karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ya kwashe dukkan zukatan dattijan mazabun da suke yankinsa cikin lokaci kankani.
Gundumar Basawa da Bomo yanki ne da suke taka rawa a wajen tsallakar da duk wani Dan takarar da yake neman kujera a karamar hukumar Sabon Gari.
Bisa wannan dalilin ne shugaban ya nunawa sauran jam'iyyu iya taku ta inda ya yi amfani da rashin cika alkawari da wakilan 'yan takara suka yi ga dattijan a wannan tsakanin.
Shugaban Honorabul Injiniya Muhammad Usman ya aike da sakon gayyata ga dukkan dattijan yankin Hayin Dogo karkashin wata kungiyar matasa da Malam Yusuf ke jagoranta a Anguwar Mangorori dake garin Samaru.
Wakilinmu ya tabbatar da zuwan duk wani dattijo mai fada aji dake wannan yankin.
Bayan halartar Dattijan ne sai shugaban ya gabatar da jawabi mai ratsa jiki tare da neman gafarar jama'a ga dukkan kurakuran da jam'iyyarsu ta APC ta yi a dukkan matakai ya ce sun tuba za a gyara da yardar Allah idan dattijan suka bayar da gudummawa a zabe mai zuwa nan da kwanaki 3 da yardar Allah.
Wani abin ban sha'awa nan take dattijan suka amince suka yi wa shugaban karamar hukumar mubaya'a tare da amincewa ga dukkan 'yan takarar shi na jam' iyyar APC baki daya.
Bincike ya nuna cewa shugaban ya yi nasarar kama zuciyar dattijan ne ta hanyar abubuwa guda biyu; na farko duk 'yan takarar da suka zo neman alfarma sukan yi wa Dattijan alkawarin wani abin kasafi amma daga karshe abin ba ya zuwa gare su sai sun sha bakar wahala.
Na biyu da yawa 'yan takarar jam'iyyu da suke zuwa neman alfarma wajen Dattijan ba su da wakilai da suka san darajar dattawan wanda shi Honorabul Injiniya ya ankare da wadannan matsalar da wakilan 'yan takarar ke da shi hakan yasa ya zo da kanshi ya durkusa gaban dattawan ya nemi alfarma kuma nan take suka ce za su yi mashi.
Malam Umar na cikin dattawan da suka halarci taron ya tabbatarwa manema labarai cewa wakilan 'yan takarar na wahalar da su don haka yasa suka amsawa shugaban karamar hukumar ta Sabon Gari kiransa domin ya nuna yasan darajarsu don haka duk abin da ya ce shi za mu yi a cewarsu.
Wannan dabara da shugaban karamar hukumar Sabon Gari ya fitar na nuna cewa sauran jam'iyyu za su fuskanci kalubale a wannan yanki na Samaru da Bomo da Basawa da kallon kura Hayin Dogo amma lokaci ne alkali bari mu zura idanu mu ga mai zai wakana a ranar fadin sakamako.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments