Wanda ya assasa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), dake Kano, Farfesa Ada...
Wanda ya assasa kuma
shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta
Nijeriya (MAAUN), dake Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika sakon ta’aziyyarsa
ga masarautar Dutse da gwamnatin jihar Jigawa bisa rasuwar mai martaba Sarkin
Dutse, Dr. Nuhu Muhammadu Sanusi.
Sanusi mai shekaru 79
ya rasu ne a ranar Talata a wani asibiti da ke Abuja bayan ya yi fama da
gajeruwar rashin lafiya.
Sakon ta’aziyyar na
kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka
mika wa manema labarai a Kano a ranar Juma’a.
Farfesa Gwarzo, wanda
shi ne har wala yau Shugaban Kungiyar Jami’o’in Masu Zaman Kansu na Afrika (AAPU)
ya bayyana cewa tabbas Jihar Jigawa ta yi babban rashin mutum mai daraja wanda
yake jagora ne da daukacin al’ummar masarautarsa ke kaunarsa saboda tawali’unsa.
Ya bayyana rasuwar
sarkin a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalansa ba, masarautar Dutse da
jihar jigawa kadai ba, har ma da kasa baki daya.
“A madadin Jami’ar
Maryam Abacha American University ta Nijeriya da Nijer, ina mika sakon ta’aziyyarmu
ga gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa bisa rasuwar Sarki.
“Allah Madaukakin Sarki
ya jikan marigayin ya kuma sanya shi a Al-Jannah Firdaus, sannan ya kuma bai wa
iyalai da al’ummar masarauta da daukacin al’ummar jihar hakurin jure wannan
babban rashi da aka yi,” inji shi.
Farfesa Gwarzo, wanda
kuma ke dauke da Sarautar Wazirin HausawanTurai, ya bayyana marigayin a
matsayin mutum mai tawali’u kuma mai son zaman lafiya, wanda ya ba da gudunmawa
sosai wajen ci gaban yankinsa.
Tuni dai aka yi
jana’izar marigayi Sarkin, wanda shi ne shugaban Jami’ar Jihar Sakkwato da ke
Sakkwato na farko, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
No comments