Babban Editanmu, Ammar Muhammad Rajab ya tattauna da mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Barista Haruna Magashi, danga...
Babban Editanmu, Ammar Muhammad Rajab ya tattauna da mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Barista Haruna Magashi, dangane da takararsu da jam'iyyarsu da kuma zaben 2023 da yake gabatowa domin jin irin shirin da suka yi da kuma mene ne ya bambanta su da sauran 'yan siyasar Nijeriya da kuma fatansu a zaben. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:
MADOGARA: Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu?
Lauya me zaman kansa, kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar African Action Congress AAC.
MADOGARA: A wannan kakar zabe ta bana ta 2023; a wanne mataki ka fito?
Na fito takarar mataimakin shugaban kasa, wanda Omoyele Sowore yake takarar shugaban kasa
MADOGARA: Ganin cewar 'yan Nijeriya suna ji a jikinsu daga 2015 zuwa yanzu duba da yadda suke kokawa, me za ku yi daban idan kuka samu dama wanda zai saukaka wa' yan Nijeriya ta fuskacin tattalin arziki?
Na'am. Lallai 'yan Nijeriya sun dandana kudarsu a hannun jam'iyyar APC me mulki ta janibobi da dama, musamman janibin Tattalin Arziki. Shi tattalin arziki abu ne me fadin gaske, kuma ya shafi abubuwa da dama. Wannan kuma ya hada har da tsaro. Don haka dole sai an samar da tsaro sannan tattalin arziki zai bunkasa. Abubuwan da muka sa gaba wajen bunkasa tattalin arziki sun hada da tsaro, noma da samar da wutar lantarki. Tsarin mu na bunkasa tattalin arziki ba shi ne kowa ya samu aiki a gwamnati ba, ko ta karamar hukumar ko jiha ko ma kasa baki daya. Za mu bayar da dama da yanayi da kowane dan kasa zai samu aikin yi da dogaro da kai ba lallai sai ya dogara da gwamnati ba. To in dai da tsaro da kasar noma kuma da wutar lantarki, duk matasan mu za su samu aikin yi wanda zai rike su. A don haka zamu bada karfi sosai kan wadannan abubuwa.
MADOGARA: Wani irin yunkuri kuka yi a yayin kamfen dinku wajen wayar da kan al'umma dangane da takararku da jam'iyyarku?
Lallai mun yunkura sosai wajen wayar da kan jama'a ta hanyoyi daban-daban wadanda suka hada da fadakarwa a gidajen talabijin da rediyo, jaridu da kuma soshiyal midiya. Haka nan mu yi yawon kamfen gari-gari, kuma muna shiga har cikin kauyuka domin wayar da kan jama'a su fito su yi zaɓe, kuma su zabi jam'iyyar AAC.
MADOGARA: Shin kuna da fatan cewa za ku iya samun nasara a zaben da za a yi?
Kwarai da gaske. Ai bamu fito takara ba sai da muka dubi yanayi da inda hankulan 'yan Nijeriya yake, muka yi nazari sosai sannan muka ga yiwuwar fahimtar da 'yan kasa su yi mu. Don haka muna da yakinin samun nasara.
MADOGARA: wasu sun cire fata a zaben Nijeriya, suna ganin 6ata lokaci ne fita ka za6i wani domin a cewarsu duk 'yan siyasa abu daya ne. Me ya bambanta ku da sauran 'yan siyasar da aka saba da su?
Lallai kuskure ne wasu mutane su kauracewa harkar siyasa da zaɓe, duk da cewa a baya an samu yanayin da wadanda al'umma ke zaba daban, wadanda ake ba mulkin daba. Amma yanzu yanayin ya sauya yadda ya zama kuri'a tana da tasiri a zaɓe.
Amma jam'iyyu da 'yan siyasa ai kowa daban yake tunda kowa yana da tsare-tsare da 'manifesto' dinsa. To wanda duk ya nazarci 'manifesto' din mu zai tabbatar da cewa tafiyar tamu daban ce da ta sauran. Don mu talakawa muka dosa gaba daya.
MADOGARA: wanne kira za ku yi ga 'yan Nijeriya dangane da zaben da za a yi a karshen mako?
Kiran mu shi ne a fito a yi zaɓe, kuma a yi zaɓe lafiya babu tashin hankali, kuma a zabi jam'iyyar AAC.
No comments