Daga Fatima Salisu, Kaduna Akalla mutane 1, 000 ne suka sami tallafin magani daga shahararriyar kungiyarnan mai suna UBA SANI NE...
Daga Fatima Salisu, Kaduna
Akalla mutane 1, 000 ne suka sami tallafin magani daga shahararriyar kungiyarnan mai suna UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS a yankin Dan Bushiya da Anguwar Keke dake a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Taron an gudanar da shi ne a wurare guda biyu. Na farko a gudanar da shi ne a Anguwar Dan Bushiya inda aka tallafawa mutane 500 sai Anguwar Keke inda aka gudanar da shi a LEA Primary Schools nan ma an bai wa mutum 500 mutane da yawa ne suka sami halarta taron bayar da tallafin a dukkan bangarori biyun.
Alhaji Ahmed Sani shi ne shugaban wannan kungiya ta UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS da yake gabatar da jawabinsa yayin kaddamar da tallafin maganin a wannan yankin ya fara ne da godiya ga Allah tare da nuna jinjina ga al'ummar da suka amsa gayyatar da suka yi musu a wannan lokacin.
Shugaban ya sha alwashin ci gaba da irin wannan hidima ga jama'a zarar jama'ar sun bayar da goyon bayansu ga dan takararsu na kujerar gwamnan jihar Kaduna a jam'iyyar APC wato Sanata Uba Sani in Allah ya kai su lokacin.
Karshe ya yi matukar farin ciki bisa yadda jama'a suke bin doka da oda yayin bayar da tallafin maganin.
Honorabul Muhammad Jalal daga Fiscal Responsibility Commission na jihar Kaduna shi ne ya zamo shugaban taron a bangaren Anguwar Dan Bushiya lokacin bayar da tallafin maganin.
A cikin bayaninsa ya sanyawa taron albarka tare da nuna goyon baya ga kungiyar da fatan alheri ga tafiyar ta su kuma ya ce in Allah ya so jama'ar wannan yanki za su ci gaba da samun tagomacin siyasa in suka bayar da goyon baya ga mutane masu manufofin kyautatawa al'umma.
Haka zalika Dakta Christy Ayi Alademerin
cikakken memba ce a Human Resources Kaduna SUBEB kuma ita ce shugaban taro kuma wakiliyar mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna a wajen taron.
Ita ma ta yi kyakykyawan jawabi a madadin mataimakiyar gwamnan na jihar Kaduna Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe.
Har wakiliyar gwamnan ta ce gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da sharewa jama'ar jihar ta hawaye da ikon Allah karshe ta yaba kokarin kungiyar tare da fatan alheri ga dukkan mutanen da suka halarci taron.
Malam Muhammad Ibrahim shi ma ya zamo bulabba cikin manyan bakin da suka shugabanci wannan tarukan bayar da tallafin.
Alhaji Muhammad Ibrahim shima ya nuna farin cikinsa da ganin yadda kungiyar ta UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS ke gudanar da aikinsu nan take ya yi fatan alheri gare su da sauran al'ummar da suka sami damar halartar taron.
Suma bangaren Sarakuna da Limaman addinai sun sami zuwa wajen taron kuma sun yi wa shugaban kungiyar ta UBA SANI NETWORK FOR PROGRESS fatan alheri da ya kawo wa jama'ar yankuna biyu Dan Bushiya da Anguwar Keke tallafin magani da fatan Allah ya taimaki tafiyar ta Dan takarar kujerar na gwannan jihar Kaduna Sanata Uba Sani insha Allahu.
Abin ban sha'awa wajalen taron shi ne yadda Sarakuna da malamai suka gudanar da jawabai na nuna jin dadinsu da kokarin kungiyar da ta kawo tallafin dukkansu sun yi fatan alheri ga shugaban kungiya bisa namijin kokarinsa da ya nuna a wannan ranar.
Bincike ya tabbatar da cewa akalla mutum 1000 ne suka amfana da tallafin maganin.
Haka zalika tallafin ya shafi gwaje-gwaje ne a bangarorin da dama tare da bayar da magani bayan tabbatar da irin lalurar dake damun wanda aka gwada.
Malam Nuhu daga Anguwar ta Dan Bushiyar na daya daga cikin wanda aka gwada har aka bashi magani shima ya yi wa Dan takarar fatan samun nasara a wannan zabe mai zuwa.
Ya zuwa hada wannan rahoton mutane da yawa suke sanyawa tafiyar neman nasarar Sanata Uba Sani bisa kokarin da kungiyoyin da ke tare da shi suke yi.
An kaddamar cikin tsari an fara cikin tsari.
No comments