Magidancin da ya rasa ransa. Daga Mustapha Muhammad A ranar Alhamis ne aka wayi gari a ƙaramar Hukumar Sabon Garin Zariya dake Jihar Kaduna,...
![]() |
Magidancin da ya rasa ransa. |
Daga Mustapha Muhammad
A ranar Alhamis ne aka wayi gari a ƙaramar Hukumar Sabon Garin Zariya dake Jihar Kaduna, a wata Unguwa da ake kira da Hayin Ojo da Ibtila'in gobara da ta kama wani gida tare da ƙone gidan da mutanen cikin gidan.
Ganau sun ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare. A yayin zantawarmu da maƙwabcin gidan, ya shaida mana cewa; wasu daga cikin ƴan Unguwar sun ce sun ji lokacin da ake ta buga ƙofar gidan, amma ba su kawo me ke faruwa ba, saboda bayan an ɗan buga ƙofar shiru suka ji can dai sai wani ya fito ya yi kururuwa a ka kawo ɗauki.
![]() |
Al'umma sun yi dafifi suna kallon gidan da gobarar ta kama. |
Ya ci gaba da cewa, bayan fitowar su sun daki ƙofar domin ta buɗe sai shokin ya kama su sai aka ce a yanke shawarar yanke wutar gidan, kafin nan kuma wutar ta yi ƙarfi tunda wutar ta nan gaban gidan ta taso sannan kuma gashi dare ne sun rasa yadda za su yi sai daga baya shawarar fasa ginin gidan ta baya ta ta zo, bayan an fasa ginin sai aka tarar da su duk sun ƙone. “Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un. Allah Ta'ala ya ɗauki abin shi dukka”.
Ya ci gaba da cewa; “Ashe lokacin da shi Maigidan ya gama buga gidan ya kasa buɗewa kasantuwar hayaƙi sai ya koma ya tattara yaran shi ya rungume su a kan gadon, ita kuma uwar ita ma ta rungume jaririyar ta sai shi kuma babban ɗan ya gudu gefen sif, wallahi dukka a haka aka same su duk sun rasu, ɗaya ne kawai yake da sauran rai shi ma kafin a kai shi asibiti ya cika”, ya tabbatar mana.
Ya ci gaba da cewa, wallahi duk wanda ya ji yadda lamarin nan ya faru sai ya yi kuka da idonsa. Allah ya gafarta musu, ya amshi shahadar waɗannan nan bayin Allah, ya yi musu addu'a. “Tabbas wannan mutuwa wa'azi ce babba ga al'ummar musulmi musamman na Hayin Ojo”, inji ganau.
![]() |
Yadda aka gudanar da jana'izar wadanda gobarar ta kashe. |
No comments