Daga Ammar M. Rajab Wani sabon rahoton da wata hukumar bincike ta SBM ta fitar ta bayyana cewa, rundunar sojin saman Nijeriya ta yi sanadi...
Daga Ammar M. Rajab
Wani sabon rahoton da
wata hukumar bincike ta SBM ta fitar ta bayyana cewa, rundunar sojin saman Nijeriya
ta yi sanadiyyar mutuwar fararen hula sama da 300 a kasar sakamakon hare-haren
da suka kira na ‘kuskure’.
A cikin rahoton mai suna
“Hatsarin Sojin Sama” da aka fitar a ranar Litinin, SBM ya ce lamarin ya faru
ne sakamakon neman maboyar 'yan ta'adda.
SBM Intelligence,
ƙungiya ce ta bincike, tana tattarawa da kuma nazarin bayanai game da abubuwan
da ke faruwa a cikin ƙasa.
Rahoton ya ce
kura-kuran sun karu a cikin shekaru biyun da suka gabata ba tare da daukar wani
kwakkwaran mataki ba daga rundunar sojojin saman ba.
SBM ta sanya jihohin
Yobe, Borno, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Zamfara, da Neja a matsayin jihohin da
suka fi fuskantar wannan bala’in.
A watan Janairu,
jaridar TheCable ta ruwaito cewa, wani hari ta sama da aka kai a garin Doma da
ke hade da jihohin Nasarawa da Binuwai, ya kashe mutane 37.
SBM ta ce lamarin shi
ne na baya-bayan nan da rundunar sojin Nijeriyar ta aikata wanda ya zama sabon salon
ayyukansu na kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba bisa ‘kuskure’.
WASU DAGA CIKIN
HARE-HAREN DA SOJOJIN SAMAN NIJERIYA SUKA KAI BISA ‘KUSKURE’
A ranar 17 ga watan
Junairun shekarar 2017, kimanin mutane 52 ne suka mutu yayin da wasu 120 suka
samu raunuka bayan da jirgin saman NAF ya kai harin bam a sansanin ‘yan gudun
hijira da ke garin Rann a jihar Borno bisa kuskure.
A ranar 13 ga Afrilu,
2020, mutane 17, ciki har da yara, suka mutu bayan da wani jirgin yakin NAF ya
kai hari a kauyen Sakotoku da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno.
A watan Afrilun 2022,
an bayar da rahoton cewa wani jirgin yakin NAF ya kashe yara shida, a lokacin
da ya harba wani bam da aka auna kan ‘yan ta’adda a kauyen Kurebe da ke karamar
hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Wasu mazauna garin 13
sun jikkata a yayin da daya ya mutu bayan wani jirgin yakin NAF ya kai hari
kauyen Kunkuna da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, a ranar 7 ga Yuli,
2022.
A watan Oktoban 2022,
Oladayo Amao, babban hafsan hafsoshin sojin sama, ya ce an fara gudanar da
bincike kan hare-haren kuskure da aka kai ta sama kan fararen hula a lokacin da
sojoji ke gudanar da ayyukansu.
Ya ce Za a samar da
matakan da za a dakile aukuwar hakan a gaba, in ji babban hafsan sojin sama.
No comments