An shiga mako na goma sha biyu al'ummar Isra'ila na gudanar da zanga-zanga mafi tsanani. Shi dai zanga-zangar al'ummar Isra...
An shiga mako na goma sha biyu al'ummar Isra'ila na gudanar da zanga-zanga mafi tsanani. Shi dai zanga-zangar al'ummar Isra'ila ne da ke adawa da kudirin gwamnati na yi wa ɓangaren shari'a garambawul ke ci gaba da gudanar da gangami a sassan ƙasar.
Wannan makon shi ne mako na goma sha biyu jere ke nan da ake gudanar da wannan zanga-zangar.
Ƴan sanda sun rufe manyan tituna a Tel Aviv inda ake gudanar da zanga-zangar.
Masu zanga-zanga sun taru a wajen gidan ministan tsaron ƙasar inda suke zarginsa da rashin ɗaukar mataki saboda tsoro bayan da aka ga kamar zai yi murabus game da batun kwanaki biyu da suka gabata.
Sojojin ko-ta-kwana sun yi gargaɗin cewa ba za su yi aiki a rundunar sojin ƙasar ba idan har aka sauya fasalin ɓangaren shari'ar suna mai cewa matakin barazana ne ga dimokraɗiyyar Isra'ila.
No comments