Jam’iyyar NNPP a jihar Kano, ta mayar wa APC mai barin gado martani game da kiraye-kirayen da take yi cewa hukumar zabe ta sake nazari kan s...
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano, ta mayar wa APC mai barin gado martani game da kiraye-kirayen da take yi cewa hukumar zabe ta sake nazari kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya bai wa Abba Kabir Yusuf (Gida-gida) nasara a zaben da aka yi da ya ba shi nasara.
APC dai ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba, kuma za ta garzaya kotu don ƙalubalantar sa.
To, sai dai shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa ya ce duk masu bai wa Dr Nasiru Yusuf Gawuna shawarar ya je kotu to kuwa so suke ya yi biyu babu.
A hirarsa da wakilin BBC a jihar Kano, Doguwa ya ce ko a jikinsu indai kan batun garzayawa kotu ne, ''Wallahi ko gezau ba mu yi ba, aje kotun mun tabbatar mu na da nasara an yi sahihin zabe, dan haka ba za mu hana kowa zuwa kotu ba.''
Ya ce takarar nan ba shi ne na farko ba, dukkan zabukan da aka yi NNPP ta na rinjaye a jihar Kano, kuma a bayyane ta ke kowa ya san APC ba ta da wani tasiri.
Doguwa ya ce ''ko gezau, ko gezau, ko gezau Abba, babu abin da ya dame mu, aje kotun mun shirya. Mun godewa jama'ar jihar Kano da suka zabi Abba, kwanann nan zai karbi shaidarsa ta cin zaben gwamna. Sannan ba mu damu ko faduwar gaba akan wannan ba, ai Kwankwaso ne jagoranmu don haka ba wani dar,'' in ji shi.
Ya kara da cewa duk ma su zuga Dr Nasir Yusuf Gawuna, ingiza mai kantu ruwa su ke yi masa, za su kai shi su baro.
''Masu zuga Gawuna ya je kotu so suke su kai shi su baro, idan an zo batun rabon mukamai a gwamnatin Tarayya, za a duba wadanda suka fadi zaben gwamna ka ga anan Gawuna da Murtala Suke Garo za a duba, amma yanzu idan sun je kotu Tinubu zai ce ban da su saboda ana kotu, anan ka ga babu wanda za a duba sai Ganduje, dan haka ya yi biyu-babu.''
Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a zaben gwamna da aka gudar a ranar 18 ga watan Mayun 2023, inda ya kada abokin takararsa na jam'iyyar APC mai mulki kuma mataimakin gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna.
Sai dai jam'iyyar APC ta ce za ta kalubalanci zaben, bi sa zargin an yi aringizon kuri'u a zaben.
No comments