Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ban Janye Takarata Ta Gwamna Ba, Inji Sani Sha'aban

  Daga Fatima Salis Kaduna Dan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar ADP, Honorabul Sani Sha'aban, ya bayyana ...

 


Daga Fatima Salis Kaduna

Dan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar ADP, Honorabul Sani Sha'aban, ya bayyana cewa maganganun da wasu ke yi cewa ya janye takararsa bai san wannan zancen ba, domin kuwa shima ji ya yi kamar almara.

Dan takarar, wanda ya bayyana cewa duka 'yan takarar da ke neman gwamna a jihar Kaduna 'yan'uwa ne domin duk daga Zazzau suka fito, ya bayyana cewa shi bai kullaci kowa ba kuma ba ya da niyyar kullatar wani a zuciyarsa.

Dan takarar, wanda ke magana a cikin wata hira da aka yi da shi ta musamman, ya bayyana maganganun janyewar ta sa har sun bata ran cibiyar jam'iyyar ta kasa, inda ya ce, "Abin har ya batawa cibiyar jam'iyyar rai har sun saki sanarwa a kan cewa ADP mai littafi babu inda ta je ta zauna ta ce dan takarar ta ya sauka."

Ya ma bayyana cewa suna ziyartar juna, ana zumunci tunda 'yan siyasa suke, amma dai ba a yi yarjejeniya da shi ba.

Dangane da nasararsa, ya bayyana cewa tafiyarsa ta riga ta yi nisa, babu abin da zai cewa Allah sai godiya, inda ya bayyana cewa jam'iyyar LP ta yi karfi a Kaduna, amma kashi 80 sun koma ADP.

Da ya ke magana dangane da salon yakin neman zabensa, sai ya bayyana cewa tafiyar 2007 daban ta ke da ta 2011, ita kuma daban ta ke da shekarar 2015, domin a misalin da ya bayar, takarar Buhari akwai lokacin da ake da Boko Haram, akwai lokacin da in za ka tafi Abuja daga Zazzau za ka dunga ganin shingayen sojoji, sai ya ce a kamfe din sa ba ya kwasar motoci masu yawa ya tafi, mutane ke bi wuri zuwa wuri da hotonsa su roki alfarma, ya kan kuma tara mutane na Unguwa a sha shayi tare ya gansu su ganshi, ba a ganin tawagarsa domin kada ya sa mutane cikin hadari. 

Dan takarar ya bayyana cewa mutane na matukar son takararsa, ana tsayar da shi a gefen titi, a wurin taro, wurin jana'iza a nuna ana so ya fito, wasu ma sun bar jam'iyyun su sun dawo tafiyarsa, inda ya ce kashi 75 na mutanen Kaduna sun yi amanna sun karanta zuciyarsa sun yarda lallai akwai wani nono da zai tarfa a garinsu.

Dan takarar wanda ya yi bayani dangane da irin wahalar da mutane ke fuskanta a bangaren karin kudin makaranta da ilimi, ya bayyana cewa fastocinsa wasu ke yi, huluna da kananan riguna, da tallarsa al'umma ke yi kuma musulmai da kiristoci.

Bincike ya nuna cewa jama'ar jihar kaduna na bashi goyon baya bisa irin taimakon al'umma da yake yi musamman matasa.

No comments