Daga Junaid Jibril Maiva Sanata mai wakiltan kudancin Borno, kuma zababben Sanata Mohammed Ali Ndume ya nuna alhini da jaje bisa...
Daga Junaid Jibril Maiva
Sanata mai wakiltan kudancin Borno, kuma zababben Sanata Mohammed Ali Ndume ya nuna alhini da jaje bisa annubar gobara daya faru a tashan Danfulani dake Biu wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka.
Cikin sakon sa na ta'aziyya da alhini, Ndume ya bayyana cewa adaidai lokaci da ake alhinin gobarar Kasuwar Monday market dake maiduguri, sai ga ubangiji ya sake jarabatar mu da wata.
Sanata Ndume yayi ta'aziyya ga iyalai, yan uwa da abokan arzikin wayen da wannan gobara ta tashan Danfulani ya rutsa da su, da musu addu'ar samun gafara da rahama.
Haka zalika Sanatan yayi ta'aziyya ga masarautar Biu da daukacin al'ummar Biu baki.
Rahotan ni sun nuna cewa an a sami tashin gobarar ne a tashan Danfulani V-Center dale karamar hukumar, inda mutane uku suka rasa rayukan su, yayin da wasu da dama sukaji rauni kuma suna cigaba da karbar kulawa a asbiti.
No comments