Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar gabanta, na ta yi ƙi amincewa da Tinubu da Kashim Shettima a matsayin...
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar gabanta, na ta yi ƙi amincewa da Tinubu da Kashim Shettima a matsayin yan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa na jam'iyyar APC a zaɓen da aka yi na 25 ga watan Fabirairu.
PDP ta nemi kotun ta juya hukuncin da mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya ya yi a ranar 13 ga watan Janairu, wanda ya ce PDP ta gaza kawo hujja kan ƙarar da ta shigar.
Cikin wani hukunci da alƙalai uku suka yi ƙarƙashin jagorancin mai shari'a James Abundaga sun yanke hukunci kan cewa PDP ta gza kawo hujja kan ƙarar da ta shigar.
Yace PDP ta shiga wani lamari ne na harkar cikin gida na jam'iyyar APC.
No comments