Daga Idris Umar, Zariya A cikin bayanai da binciken da muka gabatar a tasirin kungiyoyi a karamar hukumar Sabon Gari da jihar Ka...
Daga Idris Umar, Zariya
A cikin bayanai da binciken da muka gabatar a tasirin kungiyoyi a karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya ya nuna cewa kungiyar PDP progressive movement ta taka rawa sosai wajen ci gaban jam'iyyar PDP a matakin kananan hukumomi zuwa jiha a wannan lokacin.
Alhaji Honorabul Abdullahi Muhammad Gambo (Finance) shi ne shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Sabon Gari Jihar Kaduna a zantawar da ya yi da wakilinmu a Zariya game da tasirin aiki a kungiya ce sai ya bayyana cewa; "Da a ce jama'a za su gane amfanin kungiyar irin PDP Progressive Movement to da sun ji dadi sosai".
Honorabul Gambo ya kara da cewa aikin da kungiyar PDP progressive movement ke yi babu abin da za su ce face godiya da da fatan Alheri gare su baki daya.
Kuma ya tabbatar cewa da ana samun kungiyoyi masu aiki irin na su to da an sami nasara fiye da nasarar da ake samu a yanzu.
Shugaban ya nuna jindadinsa akan kokarin da suke yi na hada kan matasa da kare mutuncin jam'iyyar a dare da rana kuma ya yi jan hankali ga matasan da su dage a kan kokarin da suke yi na kawowa jam'iyyar ci gaba.
Alhaji Yunusa (Boy) cewa ya yi gaskiya babu abin da zai ce a game da kokarin da matasan PDP progressive movement ke yi face godiya da jinjina garesu baki daya.
Karshe ya nuna irin kokarin da suke yi shi ke kawowa jam'iyyar PDP nasarori a bangarori da dama hakan yasa ya yi masu fatan alheri tare da godiya ta musamman.
Shin ko me yasa ake yabawa wannan kungiya ta PDP Progressive movement a sako da lungu na jihar Kaduna?
Matashin Basarake kuma mai kishin matasan Danmahawayi baki daya wato Kwamared Sadik Abubakar Danmahawayi (Sadaukin Danmahawayi) cewa ya yi abubuwa da yasa kungiyarsu take gudanar da aikin daidai da abin da ake so shi ne suna kishin matasa ne tare da nema masu tsari mai inganci a tafiyar siyasar wannan zamanin don haka yasa ake yabonsu a siyasance shima godiya ya yi bisa yadda ake ba su goyon baya a kasa baki daya.
Daya daga cikin jagororin tafiyar kungiyar mai suna Shehu Hasan (Giwa) ya amsa tambayar wakilinmu akan kokarin da kungiyar ta su ke yi wajen samowa jam'iyyar PDP nasara a halin yanzu.
Kwamared Shehu ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu kashi dari na matsalolin da matasan PDP ke fuskanta saura kashi (10) duk kokari ne na PDP progressive movement da hadin kan iyayen jam'iyyar baki daya, matashin ya ce, suna godewa da yasa suke samun wannan nasarar.
Karshe matashin ya yi godiya ga dukkan membobinsu bisa yadda suke bai wa kungiyar goyon baya.
Kwamared Bashir Matawalle shi ne National Coordinator na wannan kungiyar ta PDP Progressive Movement a nasa jawabin ya yi godiya ne game da ayyukan 'ya'yan kungiyar bisa fadakar da kan matasa wajen gudanar da siyasa mai tsafta a jihar Kaduna da kasa baki daya.
Kuma ya yi albishir ga matasa cewa da ikon Allah matasa za su sami canji rayuwa a wannan gwamnati mai zuwa bisa yadda suka bayar da goyan baya na samun nasarori a wurare masu dama.
Karshe ya mika sakon murna a madadin 'ya'yan kungiyar na samun nasara ga daya daga cikin matasansu Honorabul Sadik Ango Abdullahi bisa samun nasarar zama Dan majalisar tarayya a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Ya ce wannan nasara ta matasa ne don haka suna godewa Allah. Kuma suna da tabbacin nasarorin da ake samu a jam'iyyar PDP a yanzu kungiyar PDP Progressive movement na taka rawa sosai cikin ikon Allah.
No comments