Hukumar gudanarwar gamayyar jami’o’in Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) da Franco-British International University (FB...
Hukumar gudanarwar gamayyar jami’o’in Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) da Franco-British International University (FBIU) dake Kaduna, da kuma jami’ar Canada da ke Nijeriya, sun jajantawa Sheikh Ahmad Gumi, babban Malamin addinin Musulunci dake Kaduna bisa rasuwar mahaifiyarsa.
Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jami’o’in, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda kwafinta aka mika wa manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Ya ce rasuwarta babban rashi ne ba kawai ga danginta kadai ba, har ma da daukacin al'ummar musulmin kasar.
Farfesa Gwarzo ya bayyana marigayiyar a matsayin babbar uwa mai tarbiyya wacce ta horar da ‘ya’yanta akan tafarkin Allah.
“Na yi matukar kaduwa da samun labarin rasuwar mahaifiyarmu, Allah Madaukakin Sarki ya gafarta mata kurakuranta, ya kuma sanya ta a Jannatul Firdausi.
“A madadin Hukumar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da Nijer, da Jami’ar Franco-British International University (FBIU), Kaduna da Jami’ar Kanada ta Nijeriya, ina mika sakon ta’aziyyarmu gare ku da iyalanku bisa wannan babban rashi”.
A yayin da yake yi mata addu’ar Allah ya jikanta da Rahama, Farfesa Gwarzo ya kuma yi addu’ar Allah ya bai wa Sheikh Gumi da daukacin iyalansa hakurin jure wannan rashin da ba za a iya kwatantawa ba.
Marigayiyar ta rasu ne da yammacin ranar Lahadi da misalin karfe 5:30, kuma tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a makabartar Unguwar Sarki da ke Kaduna.
Allah ya jikanta da Rahama yasa ta huta, amin.
No comments