A cikin jawabinsa na tausasawa, Tinubu ya nemi goyon bayan dukkan ‘yan Nijeriya ‘Zuciyata da kofata a bude suke gare ku’ -Faduwa zabe ba ...
A cikin jawabinsa na tausasawa, Tinubu ya nemi goyon bayan dukkan ‘yan Nijeriya
‘Zuciyata da kofata a bude suke gare ku’
-Faduwa zabe ba dalili bane na yanke kauna
Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nemi ‘yan Nijeriya da su binne duk wani rarrabuwar kai na siyasa da na kawuna domin yin aiki tare wajen gina wannan kasa mai girma.
Da yake jawabi bayan shi da zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, sun karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da yammacin ranar Laraba, Tinubu ya ce dole ne a ajiye bambancin siyasa domin gina kasa.
Tinubu ya ce bai kamata a kalli nasarar da ya samu a matsayin na kashin kai ba, yana mai jaddada cewa idan ana son samun ci gaba, dole ne dukkanin ‘yan Nijeriya su hada hannu domin su fuskantar ayyyukan dake gaba.
“Zuwa gare ku al’umma, musamman ma matasa, zan yi aiki ba dare ba rana, zan yi iya bakin kokarina wajen ganin Nijeriya ta gyaru.
“Domin wannan ya kasance nasara, ba zai zama nasara ce kawai ga mutum daya ba ko kuma ma jam’iyya daya ba. Dole ne ya zama nasara ce ga daukacin ‘yan Nijeriya wadanda suka jajirce domin kishin al’umma.
“Na san cewa da yawa ba su zabe ni ba, sannan kuna cike da takaicin yadda dan takararku bai kasance a inda nake a yanzu ba.
“Na fahimci damuwarku da kunar zuciyarku. Ga sakona zuwa gare ku, ina mai rungumarku cikin salama da tausasa zuciya daga iyali zuwa iyali.
“Wannan babban aiki da ake kira Nijeriya ya doru ne akan dukkaninmu. Aiki ne mai girma da ya girmi duk wani rarrabuwar kawuna na siyasa muhimmanci.”
Zababben shugaban kasar ya kuma bukaci magoya bayansa da su tausashi zuciyar ‘yan Nijeriyar da dan takararsu ya rasa damar yin nasara a wannan karon tare da ba su shawarar da ka da su daina kishin kasa.
“Ina rokon ku da kada ku bari abin takaicin da ya faru da ku a wannan lokaci ya hana ku ganin ci gaban kasa mai dimbin tarihi da za mu iya samu ta hanyar hada karfi da karfe wajen ganin an kawo wa kasar da muke cikinta ci gaba,” inji shi.
Da yake tsokaci kan takarar, Asiwaju Tinubu ya ce: “Hanyar tana da tsayi, amma duk da haka mun bi ta, an kuma gwabza yakin, amma mun yi nasara.
“Amma abu mafi mahimmanci, na fahimci cewa ni kawai bawa ne na cimma babbar manufa. Kun gani, wannan ya wuce batun takardar da ke tabbatar da kyakkyawan sakamakon zabe.
“Wannan muhimmin takardar tana dauke ne da alamar ci gaban dimokuradiyyar mu baki daya, har ma da buri mafi girma. Tana wakiltar mika wani aiki mai girma da kuma amana daga mutum zuwa wani mutum.
“A mafi daukakarta, wannan takardar shaidar tana kuma nuni da cewa kowannen ku yana da ikon cimma abin da wasu ke ganin ba zai yiwu ku cimma ba.”
A yayin da yake jinjina wa matasan Nijeriya, Tinubu ya bukace su da su ci gaba da kasancewa cikin fata da kuma yin aiki tukuru domin ci gaban kai da na kasa.
“Nan ba da jimawa ba, wannan kasar za ta shaidi matashin da zai tsaya a gabanku yana mai rike da wannan shaidar ta dimokuradiyya da shugabancin kasa. Za mu kuma ga wata mace ta tsaya a gabanku, tana rike da wannan takardar shaidar a matsayin mallakinta. Za mu kuma shaidi wani daga wata kabila da jama’a da dama suka yi Æ™oÆ™arin watsi da su da cewa bai cancanta ba a wannan babban mukami.
“Ta hanyar aiki tuÆ™uru, Æ™udiri da kuma Æ™waƙƙwaran imani cikin kyautata aiki, za ku iya cimma mafi kyawun abubuwa.
“Akwai matasa da suke saurarena a daidai wannan lokaci wadanda wata rana sune za su zama shugabannin wannan kyakkyawar jamhuriyyar dimokuradiyyarmu ta musamman."
Ofishin kafar watsa labarai na Tinubu
Abdulaziz Abdulaziz
Maris 1, 2023
No comments