*Ya Mika Sakon Ta’aziyyarsa Ga Sheikh Gumi, da Iyalan Abacha Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-ha...
*Ya Mika Sakon Ta’aziyyarsa Ga Sheikh Gumi, da
Iyalan Abacha
Zababben shugaban kasa
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga da
wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai a karamar hukumar Maru ta jihar
Zamfara da kuma garin Maigari na karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano a
karshen mako.
An bayyana cewa an
kashe jami’in ‘yan sanda na yanki (DPO), Sufeto na ‘yan sanda da kuma dan banga
a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara. A harin na Kano wasu ‘yan bindiga
da ba a san ko su wane ne ba sun shiga gidan wani Basarake inda suka harbe shi
har lahira.
A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar a ranar Litinin, wanda Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu, Tinubu ya ce harin da aka kai a garin Maru bayan an samu zaman lafiya na wani lokaci a jihar Zamfara, tunatarwa ce cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya.
“A matsayinmu na kasa
dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan mutane masu kisa da ta’addanci a
lokaci daya. Kashe-kashen rashin hankali da ta’addanci irin wannan bai kamata ya
samu wurin zama a kasarmu ba,” inji shi.
Zababben shugaban kasar
ya jajantawa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, da gwamnatin jihar
Zamfara da iyalan jami’an tsaron da abin ya shafa.
Tinubu har wala yau ya
kuma bukaci a gudanar da bincike kan kisan Hakimin Maigari a Jihar Kano, wanda
shi ne mahaifin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Munir Dahiru Maigari.
Ya mika ta’aziyyarsa ga
shugaban karamar hukumar, gwamnatin jihar Kano da kuma iyalan mamacin bisa
mummunan kisan da aka yi wa shugaban na al’umma.
A cikin wani sakon
ta’aziyya ta daban, zababben shugaban kasar ya jajantawa fitaccen malamin nan
Sheikh Ahmad Gumi wanda ya rasa mahaifiyarsa, da kuma iyalan Marigayi Janar
Sani Abacha bisa rasuwar dansu Abdullahi.
“Akwai ta6a zuciya rasa
masoya, komai shekarunsu kuwa. Ba za mu yi jayayya kan hukuncin Allah ba sai
dai kawai mu yi addu’a Allah Ta’ala ya jikansu da Rahama, ya kuma ba mu hakurin
jure rashinsu,” inji shi.
Zababben shugaban kasar har wala yau ya kuma jajantawa dukkannin iyalan da suka rasa ‘yan’uwansu tare da yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
No comments