Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rashin dattijon kasa, Alhaji Musa Musawa. An haife shi ne a rana...
Zababben shugaban kasa
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rashin dattijon kasa, Alhaji
Musa Musawa.
An haife shi ne a ranar
1 ga Afrilu, 1937, marigayin ya kasance mai yada labarai, jami'in diflomasiyya
kuma hazikin dan siyasa. Ya rasu ne a ranar Talata bayan ya sha fama da rashin
lafiya.
Alhaji Musa Musawa ya
rasu ya bar ‘ya’ya da dama da sauran ‘yan’uwa da suka hada da mataimakiyar mai
magana da yawun kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC,
Barista Hannatu Musawa.
A cikin wata sanarwa da
aka fitar da yammacin ranar Talata daga ofishin yada labaransa, wanda Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu, Asiwaju Tinubu
ya bayyana marigayin dan jihar Katsina a matsayin daya daga cikin ‘yan gwagwarmayar
neman ‘yancin kai na Nijeriya.
“Hakika shi mutum ne
mai zurfin tunani da son ci gaba. Tun yana matashi ya hada karfi da karfe tare
da takwarorinsa masu ra’ayi daya a rusasshiyar kungiyar ‘Northern Elements
Progressive Union (NEPU)’ wajen fafutukar kwato ‘yancin kai tare da kwato
‘yancin jama’armu baki daya.
“A shekarun baya bayan
samun ‘yancin kai, Alhaji Musa Musawa ya ci gaba da hada kai da kungiyoyi dake son
kawo ci gaba a ciki da wajen siyasa domin ciyar da talakawa da wadanda ake
zalunta gaba a cikin al’umma.
“Ya kasance dan siyasa
mai son ci gaba wanda ya sauke nauyinsa a matsayinsa na mai kishin kasa. Nijeriya
ta yi rashin hazikin danta kuma za mu yi kewar shawararsa ta uba a lokacin da
muka fi bukata,” in ji Tinubu.
Zababben shugaban kasar
ya roki Allah madaukakin Sarki da ya gafartawa Dattijon da ya rasu kurakuransa,
ya kuma bai wa iyalansa hakurin da ake da bukata a lokacin bakin ciki.
No comments