Wasu 'yan bingida sun kashe Musa Mairimi, wanda ke lura da cocin ECWA da ke ƙauyen Buda a ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna. &...
Wasu 'yan bingida sun kashe Musa Mairimi, wanda ke lura da cocin ECWA da ke ƙauyen Buda a ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.
'Yan bindigar sun kuma sace matar Fasto din da suka kashe.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wani mutum da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar mata da faruwar lamarin.
Ya ce lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis.
Jaridar ta ce ta yi ƙoƙarin kiran kakakin 'yan sandan jihar Muhammed Jalige domin jin ta bakinsa amma abin ya ci tura, wayarsa a kashe.
No comments