Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zan shiga na fita wajen ganin na nemo ma da Matasa ayyukan yi a Majalissa -Hon. Aminu Ahmad Chindo

A jawabin godiya da zaɓaɓɓan dan majalissar wakilai Hon Aminu Ahmad Chindo (Sadaukin Katsina) wanda zai wakilci karamar hukumar ...A jawabin godiya da zaɓaɓɓan dan majalissar wakilai Hon Aminu Ahmad Chindo (Sadaukin Katsina) wanda zai wakilci karamar hukumar katsina a Majalisar wakilai Dake Abuja.

A cikin Jawabin nasa Chindo yace Zaiyi anfani da wannan damar daya samu wajen ganin ya magance matsalolin dasuka Addabi karamar hukumar dama jahar baki daya.

"Zamu inganta tsaro ciki da wajen karamar hukumar katsina, dun ganin mutane sunci GABA da walwala yadda ya kamata"

Ya Kara da cewa zai samar ma da Matasa ayyukan Yi, wajen ganin an rage zaman kashe wando, hakan zai rage yawaitan ta'addanci a jahar.

"Zan shiga in fita wajen ganin na nemo ma da Matasa ayyukan yi a Majalissa"

Daga karshe Chindo ya roki al'umma da su zaba masa Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke domin nasamu damar da zan yi aiki Yadda ya kamata.

©Katsina City News

No comments