Daga Muhammad Farouk Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; almajiran Sheikh Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi dake garin Bauchi, sun bayyana ...
Daga Muhammad Farouk
Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; almajiran Sheikh Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi dake garin Bauchi, sun bayyana cewa su a shirye suke su mutu da wani abu ya taba farcen Malaminsu. Malam Abdallah shi ne wanda ya bayyana hakan a madadin almajiran Shehin Malamin a daren jiya Juma’a a Masallacin Malamin dake Bauchi.
A yayin da Malam Abdallah ke wannan bayanin, almajiran Shehin Malamin dake cikin Masallacin sun rika kwantsama kabbara suna mai jaddada abin da Malam Abdallah ya fadi a yayin da Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ke gefe yana saurarensu.
Malam Abdallah ya ci gaba da cewa; “duk wanda ya ci mutuncin Malam, na rantse da Allah rigimar addini ce za ta barke wacce babu ranar da za a toshe ta”, nan take mahalarta a masallacin suka barke da kabbara mai karfi.
“Ba wani dan sanda da ya kira, Ubangiji ne kawai ya sanya min a raina cewa mutanen nan wulakantaka suke son su yi. So suke su tozartaka”, inji Malam Abdallah a gaban Dr Idris Dutsen Tanshi.
A don haka Malam Abdallah ya tabbatar da cewa Malaminsu Dr Idris Dutsen Tanshi ba zai halarci zaman tattaunawar da hukumar shari'a ta jihar Bauchi ta shirya ba. Ya kuma tabbatar da cewa fahimtar Malamin na su ita ce akidarsu.
Dr Idris Dutsen Tanshi har wala yau a jawabinsa a wannan dare a gaban almajiran na shi ya yi zargin cewa ana shirin kai shi gidan yari da rusa masa masallacinsa, inda ya ce; “ya ce wallahi Malam abin da ake nufi da maganar mukabala din nan; bayan mukabala ana son a kama ka. Bayan an kama ka za a kai ka kotu, ana kai ka kotu, Alkalin zai tura ka gidan gyaran hali, idan ya tura ka gidan gyaran hali daga baya masallacinka za a rusa shi”, inji shi a lokacin da yake labarta abin da wani ya gaya mishi.
Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS) reshen jihar Bauchi ta ce ta janye halartar zaman da za a yi da Dr. Idris Dutsen Tanshi, tana mai cewa; kamata ya yi a yi wa Malamin nasiha idan ana ganin ya yi amfani da wasu lafuzan da bai kamata ba. Domin a cewar JIBWIS zantukan Malamin kan Manzon Allah (S) batu ne da ya shafi akidarsu.
Iliyasu Danjuma Bandas, Sakataren JIBWIS na Bauchi shi ne ya tabbatar da hakan a takardar da ya aikewa da Hukumar Shari’a ta Bauchi kan batun janyewarsu daga halartar zaman tattaunawar.
“Da fatan z aka fahimce mu, kuma Allah ya yi mana kyakkyawan jagora, Amin”, a cewar bayanin takardar.
Sai dai a wata sabuwar sanarwa da Hukumar Shari’a ta Bauchi ta fitar, wanda shugabanta Ibrahim Musa Yisin ya sanyawa hannu ya ce sun dage zaman shari’ar a yau Asabar 8 ga watan Afrilu, za su sanar da sabuwar ranar da za su yi zaman tattaunawar.
“ina mai sanar da kai a hukumance cewa an sauya ranar gabatar da wannan tattaunawar kamar yadda aka tsara a ranar 8 ga watan Afrilun 2023.
“Za mu sanar da kai sabuwar ranar da za a sanya yadda ya dace”, sanarwar ta tabbatar.
Bayan sun tabbatar da cewa gaggan Malami da almajirai ne masu goyon bayan Dr Idris Dutsen Tashin daga bangaren Izala da Salafiyya suka dira a masallacin Malamin domin ba shi kariya tare da jaddada goyon bayansu ga kalaman Malamin.
Dr Idris Dutsen Tanshi dai a yayin da yake mayar da martani kan wani waken yabo na fiyayyen halitta da wasu ‘yan wasan Hausa suka yi wanda aka fi saninsu da ‘yan Kannywood, Shehin Malamin ya ce; "Kai! Na Manzon Allahn ma ba mu son taimakonsa karewarta ke nan".
Wannan kalma kadai ta sanya Hukumar shari’a ta Bauchi ta aika masa da takardar gayyata ta tattaunawa domin ya fayyace abin da yake nufi. Takardar ta fara da cewa; “Bisa umurni ina rubuto maka gayyata a hukumance zuwa ga wata tattaunawa (munakasha) domin karin bayani kan wasu kalamai da ka yi a lokacin Tafsirin Ramadan idan ka ce; “Kai! Na Manzon Allahn ma ba mu son taimakonsa karewarta ke nan".
Takardar ta ci gaba da cewa; “Gamsasshen karin bayaninka zai taimaka wajen rage tashin hankalin da al'ummar Musulmi ta fada (sakamakon kalamanka), tare da samar da dawwamammen zaman lafiya a tsakanin al'ummar Musulmi".
Wannan dai kalamai na Dr Idris Dutsen Tanshi ya tada hazo idan al’ummar Musulmi da dama suke kallon wannan a matsayin raina Manzon Allah (S) da batanci gare shi tare da rashin ladabi da munana zance kan Annabi (S).
No comments