Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

''Ɗaliban Nijeriya A Sudan Na Cikin Tsaka-Mai-Wuya''

  Dubban dalibai 'yan Najeriya da ke karatu a Sudan na ci gaba da kokawa game da tashin hankalin da suke ciki saboda yaƙin da ake ci gab...

 


Dubban dalibai 'yan Najeriya da ke karatu a Sudan na ci gaba da kokawa game da tashin hankalin da suke ciki saboda yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa a Khartoum, babban birnin ƙasar.

Sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF masu kayan sarki sun shafe sama da mako ɗaya suna yaƙar juna, lamarin da ya jefa fararen hula da dama cikin wahalhalu.

Cikin waɗannan fararen hula har da ɗalibai 'yan Najeriya, kuma suna ta kiraye-kiraye gwamnatin ƙasarsu ta kai musu ɗauki a kwashe su zuwa gida.

Ɗaya daga cikin ɗaliban Fauziyya Idris Safiyo, wadda ta samu damar tsallakawa daga birnin Khartoum zuwa garin Gallabat da ke kan iyakar Sudan da ƙasar Habasha ta ce lamarin ya fara fin ƙarfin mutane.

"Muna jin harbi ta sama da kasa ana ruwan bama-bamai, jirage suna ta harbi, babu abinci, babu ruwa, babu magani. Ba a iya tafiya, babu kuɗi, kuma ɓata-gari sun yi yawa" in ji Fauziyya.

Ɗalibar ta ce Ƙasashe da dama sun fara kwashe mutanensu, amma babu wani labarin kwashe 'yan Najeriya.

"Mu 'yan Najeriya ne kaɗai muka rage, kuma akwai mata da yawa a cikinmu, mahukuntan wasu ƙasashe maƙwabtan Sudan kamar Habasha ba sa bari 'yan Najeriya su shiga ƙasashensu sai da biza" a cewar ɗalibar.

Da yake ƙarin haske kan halin tsaka-mai-wuya da suke ciki shi ma Muhammad Nura Bello, Shugaban ɗaliban Najeriya a jami’ar Sudan International University ya ce babu wutar lantarki, sannan kuma 'yan gari ma na tserewa.

"Mafi yawan ɗalibai sun damu matuƙa domin wasu abincinsu ya ƙare, sannan za ka ga 'yan gari ma suna tserewa" a cewarsa.

Ya ce da suka tuntuɓi ofishin jakadancin Najeriya a Sudan ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an kwashe su, to amma har yanzu hakan bai tabbata ba.

Nura ya ce jin shiru daga hukumomin Najeriya ne, ya sa ɗaliban suka kasa gamsuwa da ƙoƙarin da gwamnatin ta ce tana yi.

Tuni, wasu ƙasashen Afirka kamar Somaliya da Kenya suka fara kwashe 'yan ƙasashensu daga Sudan.

Faɗa ya kaure ne a tsakanin rundunonin sojoji biyu na Sudan waɗanda a baya abokan ƙawancen juna ne.

No comments