Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Amurka Ta Kwashe Jami'anta A Yayin Da Rikici Ya Kazanta A Sudan

  Daga Ammar M. Rajab Kasar Amurka ta kwashe jami'an ofishin Jakadancinta da iyalinsu daga babban birnin kasar Sudan wato Khartoum a yay...

 


Daga Ammar M. Rajab

Kasar Amurka ta kwashe jami'an ofishin Jakadancinta da iyalinsu daga babban birnin kasar Sudan wato Khartoum a yayin da rikici ke kara kazanta tsakanin sojojin kasar da rundunar RSF. 

Kafar watsa labaran Press TV ta labarto cewa sojojin Amurka sun kwashe akalla jami'an Amurka guda 70 daga birnin na Sudan a ranar Lahadi a yayin da suka rufe ofishin Jakadancinsu na sai mama ta gani bayan da suka dauke jami'ansu na karshe daga ofishin. 

Kwashewar gaggawar da dakarun Amurka na musamman 100 suka yi, ya dauke su kasa da sa'a guda, ba tare da samun asarar rai ba.

Jirage masu saukar ungulu na MH-47 guda uku sun kai ma'aikatan ofishin jakadancin zuwa wani wuri da ba a bayyana ba a kasar Habasha.

Sai dai duk da haka, dubban Amurkawa masu zaman kansu sun kasance a Sudan, inda jami'an Amurka suka ce yana da matukar hadari a gudanar da wani gagarumin aikin kwashe mutane.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya godewa sojojin kasarsa da suka gudanar da aikin, yana mai cewa an kammala aikin kwaso jami'an gwamnatin Amurka daga birnin Khartoum cikin nasara.

Biden ya ba da umarnin kwaso ma’aikatan ofishin jakadancin ne bayan da ya samu tabbaci a ranar Asabar daga masu ba shi shawara kan harkokin tsaron kasar cewa fadan ba zai lafa ba a yanzu.

Ya kuma godewa Djibouti, Habasha, da Saudi Arebiya, wadanda ya ce sun taka muhimmiyar rawa wajen "nasarar aikinmu."

Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa yana samun rahotanni akai-akai daga tawagarsa kan kokarin taimakawa sauran Amurkawa a Sudan "gwargwadon iko."

Ya kuma yi kira da a kawo karshen tashin hankalin a kasar ta Afirka, yana mai cewa dole ne bangarorin da ke gaba da juna su aiwatar da shirin tsagaita wuta cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba, su ba da damar gudanar da ayyukan jin kai ba tare da wata tangarda ba, sannan su mutunta ra'ayin mutanen Sudan.

Tun da farko a ranar, RSF ta yi iƙirarin "ta haɗa kai da sojojin Amurka domin kwasar jami'an diflomasiyya da iyalinsu.

Sannan Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Bass ya musanta wannan ikirarin, yana mai cewa "sun dai ba da hadin kai har ta kai ga ba su bude wuta ga jami'anmu ba a yayin gudanar da aikin."

An gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da na RSF a ranar 15 ga watan Afrilu a daidai lokacin da aka samu sabani kan shigar da masu aikin jin kan a cikin sojojin.

Fadan dai ya kawo cikas ga sabon shirin mika mulki ga gwamnatin farar hula, shekaru hudu bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir da kuma shekaru biyu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

No comments