Daga Ammar M. Rajab Shekaru bakwai da kisan 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a...
Daga Ammar M. Rajab
Shekaru
bakwai da kisan 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky wadanda aka
fi sani da ‘yan shi’a fiye da dubu daya a Disambar 2015, daga karshe an bai wa
masu ababen hawa daga cikinsu kayansu.
A
ranar Asabar 1 ga watan Afrilun 2023 aka bai wa ‘yan shi’ar motocinsu da
baburansu da Keke Napep bayan da wata babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin
hakan bayan kwashe tsawon lokaci ana tafka shari'a.
Sai
dai da yawan motocin an farfasa su da harsasai. A yayin da wasu motocin da aka
damkawa 'yan sanda ajiyarsu suka sace injinansu, batiransu, tayoyinsu,
rima-rimansu da dai sauran su.
Barista
M. Abu, lauyan dake wakiltar ‘yan shi’ar a yayin ganawa da manema labarai cikin
harshen Ingilishi, ya bayyana cewa; sun zo ofishin ‘yan sanda na MTD ne bisa
hukuncin kotu da suka samo a madadin wadanda suka shigar da kara; “wato Harkar
Musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a. Mun samu hukuncin kotu
kan a sakar musu ababen hawansu daga babbar kotun Kaduna. Mun zo nan ne domin
tabbatar da an bi wannan hukuncin”, inji shi.
![]() |
Barista M. Abu a yayin da yake yi wa 'yan jarida bayani. |
Lauyan
da ya tsayawa ‘yan shi’ar a kotu ya ce bayan abin da ya faru tsakanin ‘yan shi’a
da sojoji a Disambar 2015, an kama daruruwan ‘yan shi’a bisa zargin tare hanya
tare da ababen hawansu; “wadanda mafi yawa aka kwashe a gefen hanya da kuma
gidan Malaminsu, Malam El-Zakzaky. Inda sojoji suka kwace musu ababen hawansu
tare da kama mutane wanda suka mikawa rundunar ‘yan sanda domin gudanar da
bincike tare da gurfanar da su domin yanke musu hukunci. An tafka shari’a wanda
a karshe dukkanin wadanda aka kama aka sake su tare da wanke su daga dukkanin
zarge-zarge”.
Ya
kara da cewa; “amma a bangaren ababen hawansu wadanda aka ajiye a MTD, kuma ba
a taba gabatar da su a gaban kotu ba a lokacin shari’a. Bayan wancan hukuncin mun
dauki matakin ganin an bayar da ababen hawan amma suka ki. Dole ta sa muka
shigar da kara kan hakan. Sakamakon hukuncin da kotu ta yanke cewa a bayar da
ababen hawan ne ya sa muka kasance a nan a yau”, ya tabbatar.
Lauyan
ya ce tun cikin shekarar 2022 kotun a karkashin mai shari’a A. A Amina ta bayar
da umurin bayar da ababen hawan. “daga lokacin da kotun ta bayar da umurni zuwa
yanzu ya dauki lokaci”, inji shi.
Lauyan
ya tabbatar da cewa; za su duba matakin da za su dauka a gaba duba da cewa
ababen hawan da aka ba su ba su kai wadanda suka shigar da kara suna nema ba.
![]() |
Daya daga cikin masu abin hawan, Sidi Muhammad Rabiu Kadaure yana yi wa 'yan jarida karin haske. |
Injiniya
Ahmad Gilima, daya daga cikin wanda ya zo karbar motarsa, ya ce; bayar da
ababen hawan ya sake fallasa irin girman zaluncin da gwamnatin shugaba
Muhammadu Buhari ta aikata musu.
![]() |
Injiniya Ahmad Gilima yana ganawa da 'yan jarida. |
Wakilinmu
ya labarto cewa; mafi yawan masu ababen hawan da aka bai wa kayansu lamarin ya
rutsa da su ne a muhallan Husainiyyah Bakiyyatullahi da kuma Gidan Shaikh
Zakzaky a Gyallesu.
Wakilinmu
da ya halarci wurin bayar da ababen hawan ya tarar da ‘yan Shi’ar da dama ne
suka hallara a ofishin 'yan sandan dake lura da tattara ababen hawa na MTD dake
karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya domin bayar da shaidar abin hawansu domin
su dauka. Inda suke cike wani takarda dauke da sa hannun Lauya kafin ba su abin
hawansu.
Daga
cikin ababen hawan akwai motocin lafiya na agajin gaggawa mallakin 'ISMA
Medical Care Initiatives' na Harkar Musuluncin wacce sojojin Nijeriya suka
kwashe a Disambar 2015 bayan sun kashe Likitoci da ma'aikatan lafiyan dake kula
da wadanda aka jikkata a yayin harin da sojoji suka kai muhallin Husainiyyah
Bakiyyatullah, Gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky a Gyallesu da kuma Darur Rahma
kamar yadda bayanai suka tabbatar.
Ado Sahifa, daya daga cikin wadanda suka bibiyi tabbatar da ganin an bayar da ababen hawan, ya tabbatar mana da cewa; sun karbi motoci 67, babura 10, Keke Napep guda uku.
Rahotanni
sun labarto cewa a cikin watan Disambar 2015 ne sojoji suka dira kan mabiya
Harkar Musulunci a Nijeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a bisa zargin tare wa
shugaban Hafsan sojoji na wancan lokaci, Laftanar Janar Tukur Bururai hanya a
Zariya. Lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.
Bayanai
sun nuna cewa bayan sojoji sun kammala kashe ‘yan shi’ar ne sai kuma suka
kwashe dukkanin ababen hawansu suka mikawa rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Gwamnatin
jihar Kaduna ta tabbatar da bizne mutum 347 a ramin bai daya, a yayin da
bangaren almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka ce an kasha musu ‘yan’uwa fiye
da dubu daya. Kungiyoyin kare hakkin Bil’adama na Amnesty International da
Human Rights Watch sun ce wadanda aka kashe sun fi adadin da gwamnati ta
ayyana.
No comments