Daga Idris Umar, Zariya A ranar Lahadi 9 ga watan Afrilun 2023 aka yi taron karawa juna sani kan aikin jarida. Taron wanda kamfa...
Daga Idris Umar, Zariya
A ranar Lahadi 9 ga watan Afrilun 2023 aka yi taron karawa juna sani kan aikin jarida. Taron wanda kamfanin YAHYA JINGLE MEDIA CONCEPT da hadin guiwar makarantar koyar da harshen turanci wato ELSA dake Zariya suka shirya ya samu halartar al'umma daban-daban.
Malam Abubakar Sadik System, Malama Halima Aliyu Balarabe, Yahaya Rayyan Jingle dukkansu 'yan jarida ne sun gabatar da jawabi lakan yadda aikin jarida yake.
Baya ga jawabai na sanin makama, an gabatar da wasu shirye-shirye da ake jin su a DITV da Alheri Rediyo wanda masu shirya shirin suka gabatar a fili mahalarta suka ga yadda ake shiryawa da gabatarwa. Hakan ya burge mahalarta kwarai da gaske.
Taron ya samu halartar da dama daga ma'aikatan Jarida haka nan mutane da yawa maza da mata ne suka halarci taron.
A karshe an yi tambayoyi aka bayar da amsa. Sannan aka rabawa masu horon shaida wanda Malam Muhammad Lawal Usman (Mai ELSA) da sauran baki suka bayar.
No comments