Jam'iyyar APC a jihar Taraba ta kori ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2023 da aka kammala David Sabo Kente kan zargin yi mata zago...
Jam'iyyar APC a jihar Taraba ta kori ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2023 da aka kammala David Sabo Kente kan zargin yi mata zagon- ƙasa.
Haka kuma jam'iyyar ta ce ta kori zaɓaɓɓen sanatan Taraba da Kudu David Jimkuta sakamakon zarginsa da ta yi da yi mata zaon-ƙasa a lokacin zaɓukan da suka gabata.
Shugaban jam'iyyar na jihar Elsudi Ibrahim ne ya bayyana a haka a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Jalingo babban birnin jihar.
Mista Elsudi ya ce daga yau Sabo Kente ya daina ɗaukar kansa a matsayin mamban jam'iyyar.
Elsudi ya jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban jam'iyyar na jihar, kamar yadda kotu ta tabbatar, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan ƙuri'ar yankan ƙauna da wasu membobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar suka kaɗa masa.
No comments