Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Bashin Da Bankin Duniya Ke Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 6

Adadin kudaden da Nijeriya ta ciyo bashin su daga bankin duniya ya kai naira triliyan 6, abin da ke nufin adadin ya karu da kaso 121.46, kar...


Adadin kudaden da Nijeriya ta ciyo bashin su daga bankin duniya ya kai naira triliyan 6, abin da ke nufin adadin ya karu da kaso 121.46, karkashin gwamnatin shugaba Buhari.

Wata mujalla da ke bincike kan kasashen da babban bankin ke bi bashi ta Economic Confidential ce ta bayyana hakan, ta cikin wani kundi da ta fitar, inda ta ce adadin kudin da gwamnatin Buhari ta ciwo bashin su cikin shekaru 7, sun kai dala biliyan 7 da miliyan 64.

Baya ga wannan kuma, adadin kudaden da Amurka ke bin Nijeriyar bashi ya kai dala biliyan 6 da miliyan 24, wato kusan Naira triliyan 2 da miliyan 900 kenan idan aka yi amfani da farashin gwamnati wurin lissafin dalar zuwa naira.  

Bayanai sun ce kasashen da biyar da bankin ya fi bin bashi sun dan rage yawan kudaden da ake binsu amma banda Nijeriya. 

Tuni dai masana tattalin arziki suka fara hasashen cewa gwamnati mai zuwa a kasar na iya fuskantar kalubalen biyan basussukan da ake bin Nijeriya idan ba a dauki matakin da ya dace wurin rage yawan cin bashin da ake yi yayin da kasar ke fama da karancin kudin shiga. 

No comments