Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da sojoji a zaben da ya gabata na gwamnoni da 'yan ma...
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da sojoji a zaben da ya gabata na gwamnoni da 'yan majalisun jiha a ranar 18 ga watan Maci domin yi masa horo saboda kalubalantar canza kudi da ya yi a kotu.
Bello Matawalle da takwarorinsa na jihohin Kano da Kaduna, Abdullahi Ganduje, da Nasir El-Rufai, sun kai karar gwamnatin tarayya ne kotun koli sakamakon shirin ta na canza kudi.
Gwamnonin guda uku duka 'yan jam'iyya mai mulki ne ta APC.
Matawalle dai ya rasa kujerarsa ne ga dan takarar gwamna a karshin jam'iyyar PDP a jihar, Dauda Lawal.
Dauda Lawal ya samu kuri'u 377,726 inda shi kuma gwamna Matawallen ya samu kuri'u 311,976.
Shi ma dan takarar a Kano karkashin jam'iyyar bai yi nasara ba, amma na Kaduna ya yi nasara.
Sai dai a cikin wata tattaunawa ta minti tara da gidan rediyon DW, gwamnan ya bayyana cewa an gargade shi cewa zaben zai iya kasancewa ba yadda ya ke so ba.
Ya bayyana cewa sama da motoci 300 cike da sojoji aka tura jihar ana gaf da za a yi zaben, inda kusan sojoji 50 suke a manyan rumfunan zabe domin yin barazana ga masu zabe a kan zaben APC.
"Muna da matsalar tsaro a Zamfara kuma mun roke su kan su turo mana sojoji amma basu turo ba. Amma kwana uku da a gudanar da zabe suka turo motoci 300 zuwa jihar Zamfara, wannan irin sojoji masu yawa inda sun turo mana ne domin mu yaki rashin tsaro da ya fi, amma lokacin zabe kawai suka turo su.
"Kuma ina fada maku, akwai sojoji sama da 50 a kowacce rumfar zabe. Sun bayyana (sojojin) cewa wadanda za su zabi APC ba za a bari su yi zabe ba. An tsorata mutane, an duki mutane saboda suna so su zabi APC. Duk muna da wadannan hujjojin a bidiyo. A lokacin da muka kira sojoji su kawo mana dauki ba su zo ba. Amma mun bar komai ga Allah." Kamar yadda gwamnan ya bayyana.
Da aka tambaye shi ko menene dalilin kawo sojojin yayin zaben, sai ya ce yana da rahoton sirri cewa an turo sojojin ne domin su yi magudin zabe.
"A lokacin da na ga sojojin, na san da abinda ya kawo su. Saboda na samu rahoton sirri a kan abinda za su yi min. Ba ni kawai ba da sauran gwamnonin da suka yi abinda bai yi daidai ba...Na'am, abinda aka ce shine mun je kotu saboda canza kudi da aka yi. Sun ce ni, Ganduje da gwamna El-Rufai za a hukunta mu daidai da abinda muka yi." Kamar yadda ya bayyana.
A yayin da aka tambaye shi me ya sa APC ta yi nasara a jihar yayin zaben shugaban kasa amma ta kasa yin nasara a zaben gwamna, sai Matawalle ya bayyana cewa ya yi murna da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, ya yi gagarumar nasara a jihar.
A kan ko zai je kotu saboda "rashin bin ka'idoji" sai ya bayyana cewa ya bar komai ga jam'iyya su yanke hukunci, ko za su je kotu ko a'a.
No comments