Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Dalilan Da Ya Sa Jami’an Tsaro Suka Tsare Peter Obi A Landan

  Daga Muhammad Farouk  Hukumomin A Landan sun tsare dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar Labour, Peter Obi bisa zarginsa da yin ba...

 


Daga Muhammad Farouk 

Hukumomin A Landan sun tsare dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar Labour, Peter Obi bisa zarginsa da yin basaja kamar yadda shugaban kwamitin yada labarai na yakin neman zabensa, Mista Diran Onifade ya bayyana.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Onifade ya bayyana cewa, Jami’an Hukumar shige da fice na na Landan ne suka ci zarafin Mista Obi ta hanyar tsare shi.

Onifade ya ce, Mista Obi ya isa filin jiragen sama na Heathrow ne da ke birnin Landan daga Nijeriya a ranar bikin Easter, 7 ga watan Afrilun nan, inda ya shiga layin tantance matafiya. Sai dai ya ce a nan jami’an suka zo suka mika masa takardar izinin tsare shi, sannan suka ce masa ya fice daga kan layin.

Ana ganin akwai wani mutum na daban wanda ke amfani da bayanai iri daya da na Peter Obi, abin da ya sa jami'an suka tsare shi domin tantance gaskiya.

"An yi masa tambayoyi na tsawon lokaci, abin da ba a saba ganin an yi wa wani mutun ba wanda ya shafe sama da shekaru 10 a kasar” . inji Onifade.

Daga bisani an saki Mista Obi bayan wasu 'yan Nijeriya da ke can birnin :Landan sun tsoma baki.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce, za ta yi wa Mista Obi jerin tambayoyi game da wata murya da ta fallasa wanda a cikinta aka jiyo shi yana neman taimakon Bishop David Oyedepo wajen shawo masa kan Kiristocin kasar don kada masa kuri’a, yana mai bayyana zaben 2023 a matsayin yakin addini.

Sai dai tuni Mista Obi ya bayyana wannan muryar a matsayin ta jabu wanda ya ce sam ba muryarsa ba ce.

No comments