Hadakar jagororin kabilar Igbo a Najeriya karkashin gidauniyar kula da harkokin ‘yan kabilar wato ISCAF ta bukaci Inyamuran da ke rayuwa a...
Hadakar jagororin kabilar Igbo a Najeriya karkashin gidauniyar kula da harkokin ‘yan kabilar wato ISCAF ta bukaci Inyamuran da ke rayuwa a jihar Lagos da su kaucewa mayar da martini dangane da hare-haren da ake kai musu a sassan jihar, lamarin da ke ci gaba da tsananta tun bayan zaben shugaban kasa na watan Fabarairu.
Kungiyar ta bukaci kasashen duniya su dauki matakin shiga tsakani tun gabanin lamarin ya juye zuwa rikicin kabilanci a jihar da ake da tarin ‘yan kabilar ta Igbo da ke kasuwanci.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce dole ne gwamnatin jihar Lagos da takwararta ta tarayya su biya ‘yan kabilar ta Igbo dukkanin asarar da suka yi sakamakon hare-haren da ake kai musu.
A cewar kungiyar ‘yan kabilar ta Igbo sun tafka asarar dukiyar miliyoyi a hare-haren da ake kai musu kan kadarorinsu a jihar Lagos.
A jawabinsa gaban taron manema labarai a birnin Owerri na jihar Imo shugaban kungiyar ta dattijan na Igbo Bishop Maglorious Enyioha ya ce ‘yan kabilar ta Igbo na fuskantar kyama a sassan jihar Lagos kawai saboda sun zabi son ransu.
Kiran na dattijan Igbo na zuwa kwana guda bayan kai hari kan shugaban Majalisa dattijan kungiyar kabilar Igbo, Chief Emmanuel Iwuanyanwu bayan wasu kalamai da ya alakanta Yarabawa da zama ‘yan jagaliyar siyasa.
No comments