Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta duk wasu harkokin jama'a masu alaƙa da tashin hankalin da ya faru a daren Lahadi da Litinin wanda har ...
Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta duk wasu harkokin jama'a masu alaƙa da tashin hankalin da ya faru a daren Lahadi da Litinin wanda har mutum biyu suka mutu.
Haka zalika, akwai ƙarin mutum shida kuma da suka jikkata a Sabon Garin-Tirkaniya da ke ƙaramar hukumar Chikun.
An dauki matakin ne bayan nazarin da hukumomin tsaro kamar ƴan sanda da sojoji da jami'an tsaron farin kaya suka yi, da kuma wani taron gaggawa tsakanin shugabannin addinai da sarakunan yankin.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ne ya bayyana haka a sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sanarwar ta ambato abubuwan da aka haramta da suka hadar da Kidan Bishi da Kidan Gala da farauta.
Gwamnati ta kuma ba da umarnin a kama duk wani mai ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Nasarawa da Sabon Garin Nasarawa.
A cewar sanarwar, an kama mutum uku da ke da hannu a tashin hankalin, wanda ya yi sanadin lalata motoci da dama da dukiya.
Gwamna Nasir El Rufai ya yaba da yadda sojoji da ƴan sanda suka yi azamar daƙile ruruwar tashin hankali a yankin.
No comments