Faisal Abbas Likoro, zababben dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar karamar hukumar Kudan. Daga Idris Umar, Zariya An kammala zaben da ...
![]() |
Faisal Abbas Likoro, zababben dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar karamar hukumar Kudan. |
Daga Idris Umar, Zariya
An kammala zaben da ba a kammala ba a karamar hukumar Kudan dake jihar Kaduna. Baturen zabe Farfesa Haruna Aminu ya sanar da Faisal Abbas a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna da kuri'u 22, 993 a jam’iyyar APC.
Haka zalika Honorabul Nura Abdulkarim na jam’iyyar PDP shi ke bin Faisal da kuri'u 22, 878 wanda hakan yasa Faisal ya yi nasara akan dukkan jam’iyyu da suka nemi takarar kujerar su takwas.
An sake gudanar da zaben ne a akwatuna guda biyar da suke a yankin Garu da Kauran Wali.
Duk da shelanta samun nasarar Honorabul Faisal alamu na nuna jam’iyyar PDP ba su gamsu da sakamakon zaben ba duba da yadda aka yamutsa hankalin juna yayin da jam’iyyar APC ta dauki wasu matakai da bai yi wa duk wani Dan PDP dadi ba.
![]() |
Ma'aikacin INEC na tantance daya daga cikin masu kada kuri'a. |
No comments