Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

FALLASA: Hujjojin Dake Bayyana Yadda Gwamna Matawalle Ya Fitar Da Makudan Kudade Kan Wasu Ayyukan Da Aka Bar Su A Yashe A Fadin Jihar Zamfara

Fassarar Muhammad A. Abubakar Wani bincike da aka gudanar kan wasu ayyukan gwamnatin jihar Zamfara mai barin gado karkashin Gwamna Bello Moh...


Fassarar Muhammad A. Abubakar

Wani bincike da aka gudanar kan wasu ayyukan gwamnatin jihar Zamfara mai barin gado karkashin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya bankado yadda aka fitar da cikakken kudade daga baitul malin jihar aka biya ‘yan kwangila kan ayyukan baban giwa.

Binciken da aka gudanar ya bankado wasu ayyuka da ba su da tushe balle makama a fadin kananan hukumomin jihar 14, inda aka bayar da ayyukansu tare da fitar da kudadensu da bayar da su ga ‘yan kwangila, amma duk da haka ko dai an yi watsi da ayyukan ko kuma ba a yi ko kusa da kammala ayyukan ba.

Gwamnatin mai jiran gado ta Gwamna Dauda Lawal, za ta fuskanci kalubale mai tsanani, musamman ma na bibiyar mutanen da ke da kamfanonin da gwamnati mai barin gado ta Gwamna Bello Mohammed Matawalle ta bai wa da kuma biyan kudaden kwangilolin.

Daga cikin irin wadannan ayyuka da gwamnatin Bello Matawalle ta kirkira shi ne ginawa da kuma gyara masaukan gwamna a kowacce karamar hukuma wanda ya lakume makudan kudade ba tare da an yi wani abin a zo a gani ba.

Wannan rahoton na kwakwaf ya binciki ikirarin cewa an gina masaukan gwamnan da ake magana a kai kuma an gyara su. Bincike ya nuna bisa ziyartar wuraren da aka ce aikin ya kammala, inda aka bankado sunayen ‘yan kwangilar da suka karbi kudaden daga gwamnatin jihar Zamfara.

Adadin kudaden da aka ware aka kuma fitar wa da kowacce karamar hukuma ya bambanta, an kuma raba ayyukan a tsakanin ‘yan kwangila daban-daban domin aiwatarwa. Abin ban mamaki shi ne yadda aka rika biyan cikakken kuÉ—i a wasu lokuta da kuma biyan fiye da kashi 90% ga wasu 'yan kwangila ba tare da kammala ayyukan ba. An kuma yi watsi da wasu ayyukan ana tsaka da yin su a wasu Æ™ananan hukumomi.

An biya wani dan kwangila mai kamfanin H3D International Concepts kudi har naira biliyan biyu, da miliyan dari da saba'in da daya, da dubu dari uku da uku (2, 171, 303, 781.50) a matsayin kudin aikin tuntuba bisa ayyukan gina wuraren bayar da magunguna guda 147 a cikin masaukai 14 na Gwamna a fadin jihar.

Gwamnatin jihar Zamfara ta saki zunzurutun kudi har Naira biliyan daya da miliyan dari biyar da ashirin da shida (1, 526, 000, 000) ga wani dan kwangila, mai kamfanin Bes Belmon Nigeria Limited domin gyara masaukan da ba a kammala ayyukansu ba tukunna dake fadin kananan hukumomi 14.

A Maradun, karamar hukumar Gwamna Matawalle mai barin gado, an saki kudi har naira 118,281, 150.00 ga Zannah Kachalla World Link a matsayin kammalallen kudin ginin masaukin Gwamna. Aikin bai kai kashi 70 cikin 100 ba duk da kwashe dukkanin kudaden daga Baitul malin gwamnati.

A karamar hukumar Anka, Gwamna mai barin gado ya amince a bada kudi har naira 118, 281, 150.00 domin gina masaukin gwamna a karamar hukumar. An sake wa É—an kwangilar mai kamfanin Ermano Global Enterprise naira 102, 313, 194.75 inda ya bi bashin naira 15, 967, 955.25.

An saki sama da kashi 80% na biyan wannan aikin. Hotunan da aka samu daga masaukin Gwamnan da ke Karamar Hukumar Anka sun nuna ana aikin, ba a kai matakin karshe na kammalawa ba, balle har a kai ga tsara ginin.

An bayar da kwangilar gina masaukin Gwamna a kananan hukumomin Kauran Namoda da Zurmi ga kamfanin SWAT Aga Constructions Nigeria Limited a kan kudi naira 236, 562, 300.00 inda aka bayar da kudin da ya kai 230, 648, 242.40 ga dan kwangilar.

Abin da ya rage a bai wa É—an kwangilar shi ne jimillar kudi naira 5, 914, 057.00. Amma duk da haka, hotunan ayyukan a kananan hukumomin biyun ba su nuna alamar kai wa kusa da matakin karshe na aikin ba duk da an biya sama da kashi 90% na kudaden ayyukan.

Shi dai wannann kamfanin dai na Bes Belmon Nigeria Limited, wanda ya karbi sama da naira Biliyan daya na kwangilar samar da masaukin Gwamnan da har yanzu ba a kammala ba, an sake ba shi kwangilar gina masaukan gwamna a kananan Hukumomin guda hudu da ya hada da Bungudu, Bakura, Talatar Mafara da Maru a kan jimillar kudi naira 473,124,600.00. An biya Naira 461,296,485.50 ga Kamfanin Bes Belmon Nigeria Limited domin gudanar da aikin. Abin da ya rage a kammala biyan kudin naira 11, 828, 114.50 ne. Ya zuwa hada wannan rahoton, ayyukan da aka bayar a waɗannan ƙananan hukumomi hudu an yi watsi da su.

Gwamnatin mai barin gado ta ba da kwangilar gina masaukin Gwamna a karamar hukumar Shinkafi ga wani A.G Almajir Multi-dynamic LTD akan kudi 118,281,150.00. An saki jimillar kudi naira 115, 324, 121.25 ga É—an kwangilar domin aikin. Bashin da ya rage za a biya shi ne 2, 957, 028.75. Amma duk da haka, an dakata da aikin duk da fitar da sama da kashi 90% na kudaden ayyukan.

An bai wa C.G.G.C Engineering Limited kwangilar gina masaukin Gwamna a karamar hukumar Gummi. Jimillar kudin domin kammala aikin ya kai naira 118, 281, 150.00 sannan kuma an saki jimillar kudi 114, 732, 715.50 ga kamfanin a matsayin biyan kudin aikin tare da bin bashin da ya kai 3, 548, 434.50. Ci gaban aikin masaukin Gwamna a Gummi bai kai kashi 80% ba kuma yanzu an yi watsi da shi duk da an biya sama da kashi 80% na aikin.

An bai wa De Ludo Store LTD kwangilar jimillar kudi naira 118, 281, 150.00 domin gina masaukin gwamna a karamar hukumar Birnin Magaji. An cire kudi naira 94, 624, 920.00 daga baitul malin jihar Zamfara inda aka bai wa dan kwangilar kudaden. Bashin da ya biyo shi ne 23, 656, 230. 00 duk da haka an yi watsi da aikin da bai wuce rabi ba.

Hakazalika, Gwamna Matawalle ya bayar da kwangila akan kudi kimanin naira 236, 562, 300.00 da sunan ‘Ruwan Dorawa’ domin gina masaukin gwamna a karamar hukumar Bakura. An saki jimillar kudi naira 167, 774, 654.73 ga dan kwangilar. Sauran kudin da suka rage a biya shi ne 68, 787, 645.27. Aikin na karamar hukumar Bakura bai kai kashi 50 cikin 100 da aka yi kuma tuni an yi watsi da shi.

Danguruf Pharmaceutical Limited ya samu kwangilar gina masaukin gwamna akan kudi naira 59, 141, 575. 00 a karamar hukumar Bukkuyum. An cire jimillar kudi naira 35, 608, 185.13 daga baitul malin jihar aka ba dan kwangilar. Kudin da suka rage na aikin shi ne naira 23, 533, 389.87 wanda har yanzu ba a fara aikin ba.

Za a ci gaba da fitar da karin cikakkun bayanai na sauran ayyukan baban giwa da gwamnati mai barin gado ta Mista Matawalle ta bayar a nan gaba kadan.

No comments