Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Farashin Kayan Abinci A Nijeriya Ya Sake Tashi A Wannan Shekara

  Hukumar Kididdiga ta Kasa a Nijeriya (NBS) ta sanar a ranar  Asabar cewa, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 22.04 ...

 


Hukumar Kididdiga ta Kasa a Nijeriya (NBS) ta sanar a ranar  Asabar cewa, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 22.04 a watan Maris daga kashi 21.91 cikin 100 a watan da ya gabata.

Ofishin kididdigar ya ce hauhawar farashin kayayyaki a watan Maris ya nuna karuwar kashi 0.13 cikin 100 idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki a watan Fabrairun 2023.

A cewar sabon rahoton hauhawar farashin kayayyaki, da suka hada da abinci ya karu zuwa kashi 24.46 a cikin watan Maris daga kashi 24.35 cikin dari a watan da ya gabata.

Haɓaka hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da tashi a cikin kasar da ke a matsayin mafi girman tattalin arziƙin Afirka, abin da ya sa bankin koli ya haɓaka farashin ruwa zuwa mafi girman darajarsa cikin kusan shekaru ashirin.

A ‘yan watannin nan ‘yan Najeriya sun fuskanci matsalar kudi da ba a taba ganin irinsa ba, sakamakon sake fasalin tsarin Naira na babban bankin Najeriya CBN.

A farkon watan Maris ne kotun kolin ta yanke hukuncin cewa dole ne babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita amfani da tsofaffin takardun kudi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba saboda mummunan tasirin manufofin.

A wani yunkuri na dakile matsalar hauhawar farashin kayayyaki a kasar, babban bankin Najeriya a watan Maris ya daga darajar bashi zuwa kashi 18 cikin dari.

Yawan hauhawar farashin kayayyaki, da tafiyar hawainiyar ci gaban tattalin arziki da rashin aikin yi na daga cikin kalubalen da Najeriya ke fuskanta yayin da sabon shugaban kasar ke shirin karbar mulki a watan Mayu.

No comments