Daga Idris Umar Zariya A cikin makon da ya gabata ne tsohon shugaban Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma Shugaban Kungiyar Dattawan...
Daga Idris Umar Zariya
A cikin makon da ya gabata ne tsohon shugaban Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya janyo hankalin 'yan jarida na kasa baki daya.
Farfesan, wanda ya yi wannan kiran yayin ziyarar da dandamalin masu wallafa labarai ta yanar Gizo reshen Zariya wato (Zaria Online Journalists Forum) suka kai masa ziyarar ta'aziyyar rasuwar abokinsa marigayi Farfesa Idris Abdulkadir da Allah ya karbi rayuwarsa kwanakin da suka gabata, ya fara ne da tambaya kamar haka.
"Shin me ya sa 'yan jarida ba sa tsayawa kyam wajen fadin gaskia yayin gabatar da akinsu?"
Shugaban ya ce abin tausayi a wannan kasar za ka ga dan jarida yana tsoron fadin gaskiya domin gudun ka da a kore shi a bakin aikinsa, ko kuma kar a kama shi, alhali aikin ya gaji dukkan matakin guda biyun.
Bisa haka ne Farfesa Ango Abdullahi ya yi kira gare su a kan su tsaya kyam wajen fadin gaskiya a bakin aikinsu. Ya ce hakan shi ne zai kawo ci gaban kasa a bangarori da dama.
Shugaban Kungiyar Dattawan Arewan ya kara da cewa akwai amana mai karfi a tsakanin al'umma kasa da 'yan jarida, bisa haka ne ya yi kira a gare su da su yi kokari wajen rike amanar juna tare da mutuncin aikinsu.
Farfesa Ango ya bayyana marigayi Farfesa Idris Abdulkadir a matsayin mutumin kirki abun koyi ga al'umma. Ya ce ya bar abubuwan alherai masu yawa da za a yi koyi da su.
Da mai magana da yawun dandamalin ke bayanin godiya da muhimman shawara da Farfesan ya bayar yayin ziyarar, Idris Umar daga Jaridar Hausa Leadership, ya bayyana shawarar a matsayin abin kauna, kuma ya yi fatan Allah ya jikan wanda aka rasa. Kuma ya yi wa rayuwar Farfesa Ango Abdullahi albarka.
No comments