Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Farfesa Gwarzo Ya Cancanci Lambar Yabo Mafi Girma Ta Kasa -Mahdi Wamakko

An bayyana cewa; wanda ya kafa jami'o'in Maryam Abacha American University dake Nijeriya da Nijer, da kuma Jami'ar F...


An bayyana cewa; wanda ya kafa jami'o'in Maryam Abacha American University dake Nijeriya da Nijer, da kuma Jami'ar Franco-British International University dake Kaduna da kuma Canadian University a Abuja ya cancanci Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta kasa mafi girman daraja. 

Wannan kiran ya fito ne daga bakin Mahdi Aliyu Wamakko, da ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, kuma Sanatan Sakkwato ta Arewa, a yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan da ziyarar da ya kai Jami'ar Maryam Abacha American University dake Kano. 

Mahdi ya bayyana cewa abin a yaba wa Farfesa Gwarzo ne bisa yadda yake bai wa ilimi muhimmanci a Nijeriya da ma Afrika baki daya, inda ya ce akwai bukatar a karrama shi da lambar yabo ta kasa domin hakan zai sake karfafa shi. "A kara karfafa shi. Shiyasa na ce tun farko wannan ya cancanci lambar yabo ta kasa. Lambar yabo mafi daraja ta kasarnan yakamata a ce an ba shi. Gaskiya ina ganin idan wannan gwamnatin ta kira Farfesa Gwarzo ya zo ta ba shi lambar yabo mafi girman daraja na kasarnan, ba a yi kuskure ba. Abin a yaba mishi ne, abin a kara karfafa shi ne. Hakan zai sake karfafa shi domin ya kara himma. Na san shima zai kara idan Allah ya yarda", inji shi. 

Tunda fari Mahdi Wamakko, ya yaba bisa yadda ya ga Jami'ar Maryam Abacha dake Kano, inda ya ce bai yi tunanin akwai wani wanda ya kawo irin wannan ci gaban ta fuskacin ilimi a Arewacin Nijeriya ba; "Wannan makaranta da na zo na gani abin a yaba ne, abin ci gaba ne. Ban yi tunanin akwai wani da ya kawo irin wannan ci gaba a Arewacin Nijeriya ko ma a Nijeriya da Afrika kamar wannan ba. A gaskiya wannan abin a yaba ma Farfesa ne da ya kawo wannan ci gaba. Babu wani ci gaba da ya fi ci gaban ilimi a duniya. Ilimi shi ne farko yanzu", ya nusasshe. 

Ya kara da cewa; “gaskiya na je jami’o’i da yawa, da jami’o’i masu zaman kansu da yawa, amma ban tunanin na taba ganin makarantar da ta kai wannan ko ta kusan wannan kayan aiki da gine-gine masu kyau ba".

Mahdi ya ce; wannan aiki ne na mai kishin kasa, kuma abin koyi ga al'umma; “wannan sai dan kasa, mai kishin kasa, mai son ci gaban al’umma ne zai yi irin wannan abubuwa. Kamar yadda na fada tun farko, shi dan kasa ne mai kishin kasa. Kuma mai son ci gaban kasa. Domin duk wanda yake zuba irin wannan hannun jari a ce har Nijer, abin ya kawo Kano yanzu. Da nake kan hanya ma na ga wani muhallin a Gwarzo. Shima na ga an riga an fara da Kaduna da Abuja, gaskiya wannan ba karamin abin a yaba bane. Fatanmu shi ne mutane su yi koyi da shi. Domin wannan abin koyi ne. Ya zama abin koyi ba wai a Arewaci ko a Kano ba, ko’ina A Afrika ya zama abin koyi", ya ce. 

Daga karshe ya nemi al'umma da su kai 'ya'yansu Jami'ar Maryam Abacha American University domin su yi karatu domin a cewarsa tsare tsare da shirye-shiryen Jami'ar ya zarce na saura. 

"gaskiya Jami’ar Maryam Abacha ta tserewa tsara da sauran jami’o’i. Mun ga wadansu kala-kala, mun ga yadda suke da tsarinsu. Amma da muka zo nan mun ga tsari na daban, shirye-shirye na daban, darussa na daban da wadansu abubuwa da babu su ma a Arewa yanzu ya kawo. Jami’ar Maryam Abacha jami’a ce da yakamata a ce duk wani mai kishin Arewa ya kawo dansa ya yi karatu", ya lurantar.

No comments