Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gbajabiamila Ya Mika Ta'aziyyar Zababben Shugaban Kasa Ga Iyalan Gwadabe, Dantata

Tawagar zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu karkashin jagorancin kakakin majalisar wakilai, Honorabul Femi Gbajabia...


Tawagar zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu karkashin jagorancin kakakin majalisar wakilai, Honorabul Femi Gbajabiamila, ya ziyarci iyalan Dattijon kasa, Alhaji Musa Gwadabe, da na hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, domin jajanta musu bisa rashin da suka yi a baya-bayan nan.

Gwadabe, wanda ya kasance dadadden abokin zababben shugaban kasa a siyasance, ya rasu ne a ranar Laraba a yayin da Alhaji Dantata ya yi rashin matarsa, Hajiya Rabi, a ranar 9 ga Afrilu.

Tawagar ta ziyarci iyalan guda biyu a lokuta daban-daban a ranar Alhamis a Kano.

Sauran mutanen da suka kasance cikin tawagar sun hada da ministan matasa da wasanni, Mista Sunday Dare; tsohon shugaban EFCC, Mallam Nuhu Ribadu; Mataimaki na musamman ga zababben shugaban kasa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Abdulaziz Abdulaziz, da kuma Hon. Bello Malabu.

Da yake jawabi a gidan Gwadabe, Kakakin majalisar ya ce rashin dan siyasar ba rashi ne kawai ga iyalansa ba idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen gina kasa.

Ya ce, Asiwaju Tinubu yana daraja alakar da ke tsakaninsa da marigayi Gwadabe dalilin da ya sa ke nan ya so ya kawo ziyarar ta’aziyyar da kan sa amma saboda wani abu da ya bijiro ya hana hakan.

Ya bayyana Gwadabe a matsayin dan siyasa mai son ci gaba kuma mutum ne mai martaba wanda ya goyi bayan zababben shugaban kasar.

Da yake jawabi ga Alhaji Dantata game da rashin matarsa, Gbajabiamila ya ce radadin rashin abokiyar zamansa za a iya samun sauki hakan ne kawai idan aka tuna da irin rayuwar da aka yi da marigayiyar.

Yayin da yake addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, Kakakin majalisar ya yi kira ga iyalan mutum biyun da su raya lamarin ‘yan'uwansu da suka rasa ta hanyar koyi da dabi’unsu.

Alhaji Aminu Dantata da Alhaji Nazif Gwadabe sun nuna jin dadinsu ga tawagar ta zababben shugaban kasa bisa ziyarar ta’aziyyar da suka kai musu, tare da addu’ar samun nasara ga gwamnati mai jiran gado.

No comments