Daga Ammar M. Rajab Wata mummunan gobara ta tashi a kasuwar ‘Yan Katako dake karamar hukumar Sabon Garin Zariya da ke Jihar Ka...
Daga Ammar M. Rajab
Wata mummunan gobara ta tashi a kasuwar ‘Yan Katako dake karamar hukumar Sabon Garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru a daren jiya Talata har ya zuwa wayewar garin Laraba. Wani ganau kuma daya daga cikin masu shaguna a kasuwar ya shaidawa Jaridar MADOGARA cewa wajen karfe 1 na dare aka shaida masa cewa gobara ta tashi a kasuwar inda cikin daren ya garzaya ya tafi.
Bayanai ya zuwa hada wannan rahoton ba su fayyace me ya jawo gobarar ba, sai dai ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa ta.
“An kira ni da misalin karfe daya na dare ta ma wuce aka shaida min cewa wuta ta tashi a kasuwar. Haka nan na buga babur dina na nufi kasuwar. Da zuwa na ga gobarar ta tashi a tsakiyar kasuwar ta 'Yan Katako haka muka shiga hidimar kashe ta", inji Usman Ibrahim, daya daga cikin masu shago a kasuwar ya shaidawa MADOGARA.
“Ko lokacin da na isa kasuwar shaguna da dama sun kone,” in ji shi.
Sai dai ya tabbatar mana da cewa motar kashe gobara guda daya ta je kasuwar domin kashe wutar wanda hakan ya taimaka. Amma duk da haka gobarar ta lakume miliyoyin dukiyoyi da ba za a iya tantancewa ba.
Musa Muhammad, wani ganau ya shaidawa wakilinmu cewa a halin yanzu babu wani mutum da zai iya kididdige yawan asarar da aka tafka sakamakon gobarar, amma ya ce akalla shaguna fiye da 150 suka kone a kasuwar.
Hukumomi dai har ya zuwa hada wannan rahoton ba su ce uffan ba dangane da musabbabin tashin gobarar.
No comments