Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Ta Damu Da Halin Da 'Yan Ƙasarta Ke Ciki A Sudan

  Gwamnatin Nijeriya ta ce jami'anta na yin iya bakin-ƙoƙarinsu tare da haɗin gwiwwar ofishin jakandancin kasar da ke Sudan, da gwamnato...

 


Gwamnatin Nijeriya ta ce jami'anta na yin iya bakin-ƙoƙarinsu tare da haɗin gwiwwar ofishin jakandancin kasar da ke Sudan, da gwamnatocin ƙasashen Sudan da Habasha domin tabbatar da kare lafiyar dubban 'yan ƙasar da ke Sudan.

Cikin wani saƙo da mai magana da yawun shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce ministan harkokin wajen ƙasar Geoffrey Onyeama ne ke jagorantar shirin wanda zai taimaka wajen fitar da 'yan ƙasar daga wuraren da ake rikici a ƙasar Sudan.

Haka kuma ofishin jakadancin ƙasar da ke Khartoum ya fitar da wata sanarwa wadda a cikin, ofishin ke kiran ɗaliban ƙasar da ke Sudan da su yi watsi da wasu bayanai da ƙungiyar ɗaliban ƙasar reshen Sudan ke yaɗawa, wanda ke kiran ɗaliban da su taru a wasu wurare uku domin kwashe su zuwa Najeriya.

Sanarwar ta yi kira ga ɗaliban da su kwantar da hankalinsu, sannan su zauna a gidajensu, yayin da ofishin jakadancin ya ce yana ƙoƙarin ganin ya kammala shirye-shiryen fara kwaso ɗaliban.

Ofishin jakandanci ya ce yana shaida wa ɗaliban cewa kwanciyar hankali da lafiyarsu shi ne baban damuwarsa.

No comments