Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Zaben 2023 Ne Mafi Karancin Tashin Hankali A Tarihin Nijeriya

  Ministan yada labarai na Nijeriya Alhaji Lai Mohammed. AFP - KOLA SULAIMON Gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cewa zaben 2023 da ya gudana ...

 

Ministan yada labarai na Nijeriya Alhaji Lai Mohammed. AFP - KOLA SULAIMON

Gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cewa zaben 2023 da ya gudana shi ne mafi karancin tashin hankali da aka taba gani a tarihin kasar.

Ministan yada labarai na Najeriyar Alhaji Lai Mohammed yayin wani jawabinsa a birnin Washington DC na Amurka ya ce zaben na bana shi ne wanda aka taba gani ba tare da tsananin tashe-tashen hankula ba a tarihin kasar, da bisa al’ada ake ganin kashe-kashen rayuka da kone-kone dukiyoyi a duk lokacin gudanar da zabe.

Ministan wanda ke halartar wani taro kan sha’anin tafiyar da mulki da nufin kawo karshen rikice-rikice a kasashe ta hanyar hada hannu da tawagar ‘yan jaridun kasa da kasa da kuma cibiyoyin ilimi da koya dabarun siyasa suka shirya a birnin New York.

A wata kebantacciyar tattauna tsakanin Lai Mohammed da jami’in cibiyar Hudson Institute da Atlantic Council da kuma Wilson Institute ministan yada labaran na Najeriya ya ce duk da cewa an samu rahoton mutuwar mutane 13 zuwa 28 yayin zaben na 2023 adadin ya zama mafi karanci da aka taba gani a kasar tun daga shekarun 1964 da 1965 da aka faro zabe lokacin da mutane fiye da 200 suka mutu.

A cewar ministan yada labaran na Najeriya, ko a zaben 1993 sai da mutane 100 suka rasa rayukansu yayinda a 1999 wasu 80 suka mutu kana mutum fiye da 100 suka yayin zabe a shekarar 2003 sai kuma wasu 200 a 2007.

Ministan ya ci gaba da cewa alkaluman da hukumomin tsaron Najeriyar ke adane da su na nuna yadda mutane 800 suka mutu yayin zaben 2011 biye da wasu mutum 100 da suka mutu a 2015 kana mutum 150 da suka mutu yayin zaben 2019.

Ministan yada labaran na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ya ce lura da raguwar alkaluman mutanen da ke rasa rayukansu yayin zabuka a kasar, hakan na nufin za a wayi gari ba tare samun rasa ran ko da mutum guda yayin zabe a kasar ba.

No comments