Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Kai Harin Bama-Bamai A Lebanon Da Zirin Gaza

  Daga Ammar M. Rajab   Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila (HKI) sun kai hari a Kudancin Lebanon da zirin Gaza a daidai lokacin da Fir...

 


Daga Ammar M. Rajab 

Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila (HKI) sun kai hari a Kudancin Lebanon da zirin Gaza a daidai lokacin da Firaministan Isra'ila ke cewa abokan gabarsu za su dandana kudarsu.

Dakarun sojin na HKI sun kai harin ne a wasu wurare a Lebanon da Gaza da sanyin safiyar Juma'a ba ya ga farmakin da 'yan sandan Isra’ila suka kai cikin masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a cikin makon nan.

Fashe-fashe masu karfi sun girgiza yankuna daban-daban na Gaza, a daidai lokacin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta ce jiragenta sun kai farmaki kan wasu wurare da suka hada da na kera makamai na Hamas da kuma wasu hanyoyin da aka haka a karkashin kasa.

Rundunar sojin HKI ta ce ta kuma kai hari kan mayakan Hamas da ke kudancin kasar Lebanon, inda mazauna yankin da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Rashidiyeh suka sanar da tashin bama-bamai uku.

No comments