Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

INEC Ta Nemi Sufeto Janar Na 'Yan Sanda Ya Cafke Jami'in Da ya Ce Binani Ta Ci Zabe

                                                                    Barista Hudu Ari Daga Ammar M. Rajab  Hukumar zabe mai zaman...

                                                                    Barista Hudu Ari

Daga Ammar M. Rajab 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta nemi Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya ya cafke Barista Hudu Yunusa Ari, kwamishinan INEC da ya ce 'yar takarar gwamna a jam'iyyar APC, Aisha Binani ta lashe zabe ana tsaka da kirga kuri'u. 

INEC ta nemi hakan ne a sanarwar da ta fitar da ranar Talata 18 ga Afrilun 2023 a shafinta na Facebook. 

INEC ta ce; a taronta na yau, 18 ga Afrilu, 2023, Hukumar ta tattauna batutuwan da suka taso daga zaben Gwamnan Adamawa inda ta yanke shawarar:

INEC ta ce; "Mun rubutawa Sufeto-Janar na 'yan sanda domin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da yiwuwar gurfanar da Kwamishinan zabe na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa; "Mun kuma bukaci Sakataren gwamnatin tarayya da ya jawo hankalin jami'an da aka nada kan rashin da'a da kwamishinan ya yi domin ci gaba da daukar mataki.

"Za a ci gaba da tattara sakamakon zaben a lokacin da jami'in tattara sakamako ya ayyana", inji INEC. 

                                           Daga dama; Aisha Binani, Gwamna Fintiri

No comments